Wani Dan Achaba ya ci dan banzan duka yayin da fada ya kaure akan wata tsohuwar N200
Daga cece kuce da jani in ja ka da ya gudana a tsakanin wata mata da Dan Achabar da ya dauketa, shaidan ya gitta, inda aka yi doke in doke ka, da yayi sanadiyyar garzayawa da Dan Achabar zuwa Asibiti cikin halin rai fakwai, mutu fakwai.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito rikicin ya samo asali ne a lokacin da wani Dan Achaba mai suna Okon Akpan ya dauki wata budurwa mai suna Titilope Fatai a babur dinsa zuwa Unguwar da take zama, inda Fatai ya bashi Naira dari biyar, akan zai bata canjin Naira dari uku.
KU KARANTA: bGaggan barayin mutane tare da yan fashi da makami su 6 sun fada tarkon Yansanda a jihar Katsina
Majiyar Legit.ng ta ruwaito cikin canjin da Okon ya baiwa Fatai akwai wata naira dari biyu da ta tsufa, don haka Fatai tace ba zata amshi wannan canjin ba, kuma tace masa lallai sai ya canja mata kudin, shi kuma yace ba shi da wata Naira dari biyun da zai canza mata shi.
Ba kawai sai gogan naka ya buga mashin zai yi tafiyarsa ba, ganin hakan ya sanya budurwa Fatai ta zabga masa mari, shi kuma yace da wa Allah ya hada ni idan ba ke ba, nan fay a shiga dukanta, ashe bai san yayi shuka a idon makwarwa bane, nan fa shima wasu matasa suka diran masa, har sai da suka sumar da shi.
Zuwa yanzu dai an garzaya da Okon zuwa wani babban Asibiti don a farfado da shi, sai dai wani Malami a jami’ar jihar Legas, Dakta Kaka Afolabi ya shawarci babban bankin Najeriya da ta janye tsofaffin kudi tare da zuba sabbi don magance ire iren rikita rikitan nan.
“Ka duba Naira 100 a yanzu, ta lalace, wasu ma wari suke yi, ga rashin karko, don haka yasa ba kowa ke amsar tsohuwar naira dari ba, wanda ke janyo rikita rikita a tsakanin masu cinikayya.” Inji Kaka.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
https://www.youtube.com/watch?v=EuHCfxU-D7E
Asali: Legit.ng