An kai wa Tawagar Sarkin Kwandere a Jihar Nasarawa hari
Mai martaba Sarkin Kwandere watau Alhaji Ahmadu Al-Makura ya tabbatar da cewa wasu ‘Yan iskan gari sun yi ma Jama’an sa rotse a Ranar Juma’ar nan da ta gabata lokacin da su ke tafiya a mota.
Mun samu labari daga Hukumar dillacin labarai na Kasa watau NAN cewa a Ranar 4 ga Watan Mayu wasu Bayin Allah su ka far ma Tawagar Sarkin Kwandere Alhaji Ahmadu Al-Makura inda su kayi barna a wajen sallar Juma’a a makon jiya.
Talakawan Garin sun kai wa Jama’an Sarkin hari ne a dalilin wani rikicin fili da ake yi. Sarkin yace mutanen sun fito ne rike da sanduna da duwatsu da wasu makamai. An dai kai hari kan Jami’an tsaro an kuma illata wasu motocin Sarkin.
Mutanen Garin sun ce ba za su bada filin su domin Gwamnati tayi gini-gine ba. Talakawan sun koka da cewa tuni dai an karbe filayen u an yi ginin asibitocin Gwamnati da kasuwanni don haka wannan karo su kace sai dai a nemi wani filin.
KU KARANTA: Wani babban ‘Dan siyasan Arewa ya fito da niyyar buge Buhari
Kamar dai yadda mu ka samu labari Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na shirin gina gidaje 100 ne a Yankin amma mutanen Garin sun ce ba za su yarda ba don haka Sarkin ya nemi a zauna da su da Mai girma Gwamnan Jihar.
Kwanaki kun ji cewa Kasar Sin watau China ta nuna cewa a shirye ta ke da ta narka kudin ta wajen gine-ginen gidajen da za ayi a Najeriya domin ganin an rage matsalar da ake fama da shi na karancin gidajen zama a fadin Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng