An sake yiwa Buratai Karamci na Gwarzon Jagora

An sake yiwa Buratai Karamci na Gwarzon Jagora

Mun samu rahoton cewa jami'ar Western Ville dake birnin San Diego na jihar California a kasar Amurka da kuma babbar mujallar nan ta Lead Times Africa, sun karrama shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Buratai.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan karamci ya zo a sakamakon jarumta, nuna gaskiya, gami da dattako a matsayin sa na jagoran sojin kasa na Najeriya.

An sake yiwa Buratai Karamci na Gwarzon Jagora
An sake yiwa Buratai Karamci na Gwarzon Jagora

A yayin wannan bikin karamci da aka gudanar a birnin Accra dake kasar Ghana, an gabatar da shugaban hafsin sojin dangane da kwazon jarumtar sa wajen jagorantar sojin kasa da kuma magance ta'addancin Boko Haram musamman a yankin Tafkin Chadi.

KARAMTA KUMA: Yanzu-Yanzu: An yiwa 'Dan Takarar shugaban jam'iyyar APC kisan gilla a jihar Delta

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wani babban kwamandan sojin kasa, Manjo Janar Enobong Udoh, shine ya wakilci Buratai a wurin bikin karamci.

A nasa jawabin, shugaban hafsin sojin ya bayyana cewa wannan karamci ya zo ne a sakamakon kwazo da kuma rawar da dakarun sojin kasar na Najeriya ke takawa a nahiyyar Afirka baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel