Tsokaci: Abubuwa 12 dake kashe aure da wuri a wannan zamanin

Tsokaci: Abubuwa 12 dake kashe aure da wuri a wannan zamanin

- Aure na yawan mutuwa a kasar Hausa

- Wasu dalilan ana iya magance su

- Hangen masana ya nuna a nan haka abin yafi kamari

Tsokaci: Abubuwa 12 dake kashe aure da wuri a wannan zamanin
Tsokaci: Abubuwa 12 dake kashe aure da wuri a wannan zamanin
Asali: UGC

Mun leka muku binciken wasu masu hangen nesa da ke ganin dalilan mutuwar aure a zamanin nan, ga kadan daga ciki:

1. Karya kafin ayi aure, dora mace ko miji kan ababen da a zahiri ba haka suke ba, kun dai san menene su, kamar dukiya, kayan alatu, maza kan yi wannan sosai.

2. Karyar ba'a sadu da wasu ba kafin auren. Mata suna wannan sosai.

3. Karya bayan aure, musamman da buya a ci amanar juna, wannan mazan sunfi yi.

4. Rashin haihuwa, wannan marasa tawakkali kanyi haka, musamman a kudancin kasar nan.

5. Duka, wannan yawanci dai mata aka fi yiwa, domin wai tunda addini ya ce ayi, sai kawai ayi ta jibgarta kamar baiwa. Wannan ya zama kauyanci gaskiya, kuma maza suka fi yi.

DUBA WANNAN: Addu'ar da 'yan ta'adda keyi kafin kai hari

6. Rashin yalwar arziki. Wannan laifin gwamnati ne da ma kuma kaddara, a yawan lokuta kuma rashin dabara da ilimi.

7. Rashin iya saduwa. Wannan kowanne na iya adawa ciki, mace ko namiji. Sai su nemi ilimin gamsar da juna. Akwai lokuta da dama da rashin lafiya kan janyo wannan.

8. Rashin dacewa da juna, ta fannin wayewa, ko ilimi, ko qiba, ko aji, ko ma zamanancewa.

9. Bullar sabbin halaye, kamar shaye-shaye, fushi, ko yawon dare. A wasu lokutan neman kanwar amarya ko kawarta.Wannan mazan ko matan kowa nayi.

10. Zama da wasu: Musamman iyaye, ko makwabta masu sa-ido, ko unguwar da ake tafka shirme, ko ma gidan haya. Wannan abin ba ga kowa bane sai mazan.

11. Nisa: Aiki, ko neman abinci kan kai mutum aiki nesa. Wannan kan jayo rashin kusanci. Anfi samunsa ga maza a arewa, ga mata a kudu.

12. Rashin fahimtar ko me aure ya kunsa, wasu sha'awa ke kaisu, saboda dama a wuya suke, wasu kuma dama auren dandano ne, wasu kuma auri saki, wasu ma kawai so suke su fita daga auren su shiga karuwanci, domin yafi kawo kudi kan abin da maigida zai bayar da safe na cefane.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng