'Albarka na sanya wa diya ta bayan da ta auri kirista' - Wani musulmin mahaifi

'Albarka na sanya wa diya ta bayan da ta auri kirista' - Wani musulmin mahaifi

- Sanatar Adamawa ta tona wahalar da ta sha don ta canja addini ta auri kirista

- Mahaifin ta ya fito ya wanke kansa, yace shima ya bar kiristanci ne a baya

- An yi ta yamadidi da batun a makon jiya a kafafen labaru da coci-coci

'Albarka na sanya wa diya ta bayan da ta auri kirista' - Wani musulmin mahaifi
'Albarka na sanya wa diya ta bayan da ta auri kirista' - Wani musulmin mahaifi

Madam Binta Masi Garba, Sanata dake wakiltar Arewacin jihar Adamawa, a baya, tace mahaifinta ya kone dukkan kayanta bayan da ta bar addinin Islama ta bi Yesu, a cewarta, 'Nasha bakar wahala daga iyaye na bayan na bar addininsu na bi Masihanci, inda suka kone dukkan dukiyata bayan da na auri kirista ina Yarinya.'

Sai dai Mahaifin nata, Tumba Garba, dattijo tsohon soja, yanzu ya fito ya wanke kansa, inda yace shi kam baya kyamar duk wani mai canja addini a dangi, domin shima da dan Kirista ne, amma ya musulunta ya bar iyayensa a Kiristanci.

A cewarsa, yayin ganawa da wata kungiyar musulmi, a yaankinsu a arewacin Adamawa, 'nayi farin ciki ranar da diyata ta kai ni na gana da shugaba Buhari, domin a baya yana mulkin soja na gwada hakan banci nasara ba'.

'Diya ta bata cimma addinin Islama ba, a kalamanta na baya, ba kuma ta bakanta min ba nayan ta bar addini, hasali ma, murna na taya ta, na kuma sanya mata albarka tare da sabon angonta, domin mu danginmu na kowa da kowa ne'.

DUBA WANNAN: Saudiyya zata kashe biliyoyin kudi kan shakatawa

Sanatar itama, tace masu adawar siyasa su yi adawa da ita, kan irin ayyukanta na siyasa, ba wai kan batun addinanci da kabilanci ba.

A yankin Adamawa har yanzu ana samun dangi dake da musulmi da kirista, kuma ba'a fiye jin kansu kamar a arewa maso yamma ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng