Wata Mata ta tarwatsa 'ya'yan Marainan Makwabcin ta a jihar Legas

Wata Mata ta tarwatsa 'ya'yan Marainan Makwabcin ta a jihar Legas

Hukumar 'yan sanda ta jihar Legas ta cafke wata mata mai shekaru 25, Kelechi Ugwu tare da gurfanar da ita gaban Kuliya bisa laifin raunata mazakutan wani makwabcin ta, Emeka Egwu a yankin Ajah na jihar ta Legas dake kudancin Najeriya.

Rahotanni da sanadin shafin The Punch sun bayyana cewa, wannan mata dai ta hau dokin zuciya wajen wannan aika-aika yayin da Emeka ya gaza biya mata bukatar ta sulhunta tsakanin ta da wani saurayin ta wanda ya kasance aminin sa.

Jaridar ta ruwaito cewa, an kwashi kwanaki na samun sabani tsakanin Kelechi da saurayin ta kuma aminin Emeka wanda ya sanya ya kauracewa zuwa ziyartar ta.

Wata Mata ta tarwatsa 'ya'yan Marainan Makwabcin ta a jihar Legas
Wata Mata ta tarwatsa 'ya'yan Marainan Makwabcin ta a jihar Legas
Asali: Depositphotos

A sakamakon damuwa ta so da kauna ta daukin karan tsana da dora akan Emeka wanda ya sanya ta fusata ta tunkare shi da barazanar ya shiga taitayin sa ko kuma ta dauki mataki.

Ganin cewa Emeka shi namiji ya yi hasashen cewa wannan mata ta fara kawo masa wargi inda tunkara ta da bambami.

A yayin haka ne Kelechi ta damko mazakutar sa kuma nutsa faratan ta har cikin 'ya'yan marainan sa wanda a sanadiyar haka ne ta fashe masa wari guda.

KARANTA KUMA: Atiku ya yabawa Hukumar INEC kan batun mahawara a tsakanin 'Yan Takara

Legit.ng ta fahimci cewa, an gurfanar da Kelechi a gaban kotun majistire dake garin na Ajah sakamakon laifin da ta aikata da misalin karfe 7.00 na yammacin ranar 12 ga watan Maris wanda ya sabawa sashe na 245 cikin dokokin jihar Legas.

Alkalin Kotun Mista L.O Kazeem, ya daga sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Mayu inda ya bayar da belin ta akan kudi na Naira dubu hamsin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng