An yankewa wani Barawon Qur'ani hukuncin Bulalai 10 a Kauyen Abuja

An yankewa wani Barawon Qur'ani hukuncin Bulalai 10 a Kauyen Abuja

A ranar Juma'a ta yau ne wata karamar kotu dake zaman ta kauyen Utako na garin Abuja, ta yankewa wani bawan Allah, Auwal Mu'azu hukuncin bulalai 10 da laifin satar Al-Kur'ani da takalmi kafa daya a wani masallaci.

Alkalin kotun Mista Abubakar Sadiq, ya sassauta hukunci kan wannan barawo sakamakon amsa laifin sa ba tare da bata kotun ba, inda ya kuma gargade shi akan kauracewa duk wani laifi da zai sanya a sake gurfanar da shi a gaban alkali.

Okagha Ijeoma, jami'ar 'yan sanda mai shigar da kara ta shaidawa kotun cewa Mu'azu ya aikata laifin ne da misalin karfe 1.30 na ranar 27 ga watan Afrilu, inda ake sa ran wannan hukunci zai zamto izina a gare shi da sauran masu hali irin na shi.

An yankewa wani Barawon Qur'ani hukuncin Bulalai 10 a Kauyen Abuja
An yankewa wani Barawon Qur'ani hukuncin Bulalai 10 a Kauyen Abuja

Ijeoma ta zayyana wa kotu wannan shaida ne sakamakon korafin wani masallaci da aka damke Mu'azu yayin da ya yi yunkurin awon gaba da Al-Kur'ani guda da kuma takalman wani masallaci.

KARANTA KUMA: Hotunan Shugaba Buhari yayin dawowar sa daga Kasar Amurka

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Mu'azu ya shiga hannu inda bayan binciken sa aka samu wannan kaya da nuna halin son banza a kansu.

Legit.ng kamar yadda jami'ar 'yan sanda mai shigar da korafi ta bayyana kotun wannan laifi ya sabawa sashe na 288 cikin tanadi na dokokin kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel