Labari mai dadi: Rundunar Yansandan Najeriya zata fara diban sabbin Yansanda 6000 a wannan rana

Labari mai dadi: Rundunar Yansandan Najeriya zata fara diban sabbin Yansanda 6000 a wannan rana

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da ranar Litinin 7 ga watan Mayu a matsayin ranar da zata fara diban sabbin Yansanda masu karamin mukami, wato Kurata da adadinsu ya kai guda dubu shida (6000), kamar yadda gidan Talabijn na Channels ta ruwaito.

Sanarwar ta fito ne daga hukumar gudanar da ayyukan Yansandan, PSC, a ranar Alhamis, 3 ga watan Mayu, inda tace za’a gudanar da harkokin daukan Yansandan ne a shelkwatar Yansanda na jihohi 36 dake fadin kasar nan, da kuma na babban Birnin Tarayya Abuja.

KU KARANTA: Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya hallaka mutane 183, mutane 215 sun jikkata

Babban daraktan watsa labaru na hukumar, Ikechukwu Ani ya bayyana cewa za’a fara tantance masu neman shiga aikin ne a ranar Alhamis, inda za’a fara da duba sahihancin takardunsu da kuma duba karfinsu.

Labari mai dadi: Rundunar Yansandan Najeriya zata fara diban sabbin Yansanda 6000 a wannan rana
Yansandan Najeriya

“Tuni mun aika ma masu neman aikin sakon gayyata, wanda ya kunshi ranakun da zasu halarci tantancewar, akalla mutane 133,324 masu sha’awar shiga aikin Yansanda ne hukumar za ta tantance, Kaduna cea jihar da tafi yawan masu neman aikin, su 6962.” Inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwito daga jihar Kaduna sai Katsina-6676, Benuwe 6474 da Neja 6409, yayin da jihar Legas ke da karancin masu neman aikin Yansanda da yawansu bai wauce 1013 ba, sai Bayelsa 1097, Anambra 1117 da jihar Ebonyi dake da mutum 1303.

Da yake ganawa da ma’aikatan hukumar, babban sakatarenta, Musa Istifanus ya gargadesu da cewa ba zasu lamunci cin hanci, rashawa da duk wata badakala ba a wannan muhimmin aiki na kasa, daga karshe ya shawarci manema aikin dasu nuna ladabi da biyayya a yayin tantancewar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel