Mutane 10,000 sun nemi gurbin da ake bukatar Mutane 600 a NDA

Mutane 10,000 sun nemi gurbin da ake bukatar Mutane 600 a NDA

- Rashin aiki da kuma wahalar samun guraben karatu a manyan makarantun kasar nan na ciga da ta'azzara

- Babban kwamandan kwalejin tsaro ta kasa ne ya shaida cewa, yawan wadanda suka nemi shiga kwalejin ya ninninka adadin da suke nema

Kwamandan kwalejin tsaro ta kasa (NDA) dake Kaduna, Maj.-Gen. Adeniyi Oyebade, ya ce, sama da Mutane 10,000 ne suka nemi shiga gurabe 600 kacal da hukama take bukata.

Kwamandan ya fadi haka ne a yau Alhamis, yayinda kungiyar yan jarida Mata (NAWOJ) reshen jihar Kaduna ta kai masa ziyarar ban girma ofishinsa.

Tsananin rashin aiki yasa Mutane 10,000 neman gurbin da ake bukatar Mutane 600 a NDA
Tsananin rashin aiki yasa Mutane 10,000 neman gurbin da ake bukatar Mutane 600 a NDA

ya kuma ce, sakamakon karancin guraben da suke bukata yasa suke tabbatarwa lallai-lallai an zabi wadanda suka cancanta domin cike guraben da suke da bukata a makarantar.

Oyebade ya kara da cewa, kwalejin haka nan siddan bata hana wadanda suke neman shiga mutukar sun cancanta ta hanyar cin jarrabawar shiga da ake gudanarwar kafin dibar daliban.

KU KARANTA: Mutuwar Wani 'Dalibi 1 ta sanya an rufe wata Jami'a a jihar Kano

Sannan kuma ya tabbatarwa da kungiyar cewa, a shirye kwalejin tasu take ta cigaba da martaba kyakkyawar alakar dake akwai tsakaninsu.

Tsananin rashin aiki yasa Mutane 10,000 neman gurbin da ake bukatar Mutane 600 a NDA
Tsananin rashin aiki yasa Mutane 10,000 neman gurbin da ake bukatar Mutane 600 a NDA

Ana ta jawabin shugaban kungiyar Mrs Juliet Oyoyo, cewa tayi, akwai matasa da yawan gaske da suke neman shiga kwalejin amma basa samun dama. A don haka ne shugabar kungiyar tayi kira ga shugabancin kwalejin da su duba yiwuwar ba su dama kasancewar kishin kasar nan yasa suke burin bayar da tasu gudunmawar domin cigaban Najeriya.

Sannan ta kuma kara da cewa, babban makasudin ziyarar tasu shi ne, neman hadin kai tare da goyon bayan kwalejin yayin taron da kungiyar zata gudanar a ranar 30 ga watan Mayu a jihar ta Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel