Borkonon tsohuwa ‘Yan Sanda su ka nemi su yi ta shakawa Dino Melaye – Ben Bruce
- Ben Murray-Bruce ya fadi dalilin da ya sa Melaye ya tsere daga motar ‘Yan Sanda
- Sanatan ya leka asibiti ya gana da ‘Dan uwan sa Dino Melaye a farkon makon nan
- ‘Dan Majalisar yace uwar-bari ce ta sa Sanata Melaye ya duro daga motar Jami’an
A jiya mu ke jin cewa wani ‘Dan Majalisar kasar nan a shafin sa na Tuwita ya bayyana asalin abin da ya sa Sanata Dino Melaye ya fado daga motar ‘Yan Sanda lokacin an kama shi ana kokarin wucewa da shi gidan kaso.
Sanata Ben Murray-Bruce na Jam’iyyar adawa PDP ya kai wa abokin aikin na sa Dino Melaye ziyara a asibiti a Ranar Litinin kamar yadda Sanatan ya bayyana da bakin sa. Ben Bruce yace bai ji dadin yadda ya ga Sanata Melaye ba.
KU KARANTA: Jirgin Shugaba Buhari ya make a hanyar Amurka
Fitacen ‘Dan Majalisar yace ainihi an fesawa Sanatan na Yammacin Kogi barkonon tsohuwa ne alhali yana da cutar ‘Asthma’. Sanatan yace ko da aka kara kokarin shakawa Sanatan borkonon sai yayi wuf ya duro daga cikin motar.
Kwanakin baya ma dai Sanata Shehu Sani ya kai wa ‘Dan Majalisar ziyara a asibiti. Ben Bruce wanda ya duba Sanatan a gadon sa a makon nan yace har ta kai borkonon tsohuwar da aka rika shakawa Melaye ya hana sa nunfashi a motar.
Ku na da sane cewa labaran da ke shigowa yanzu na nuna cewa Kotun Majistare da ke zaune a Lokoja inda aka gurfanar da Sanata Dino Melaye da safen nan ta hana shi beli.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng