Ajali ya Katse Hanzarin Wani Matashi da ya sha ƙwayar Tramol a jihar Benuwe

Ajali ya Katse Hanzarin Wani Matashi da ya sha ƙwayar Tramol a jihar Benuwe

Mun samu rahoton cewa wani matashi mai sunan Etim da shekarun sa ba su wuci 20 a duniya ba, yayi gamo da ajalin sa bayan ya sha ƙwayar Tramol kuma tai masa karo a yankin Otukpo na jihar Benuwe a Arewacin Najeriya.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, an garzaya da Etin wanda ya shara da sunan Ratty zuwa asibitin Abba Clinic dake hanyar Ogiri bayan ya afa muggan kwayoyin kuma ya fice daga cikin hayyacin sa nan take a ranar 30 ga watan Afrilu.

Ajali ya Katse Hanzarin Wani Matashi da ya sha ƙwayar Tramol a jihar Benuwe
Ajali ya Katse Hanzarin Wani Matashi da ya sha ƙwayar Tramol a jihar Benuwe

Kamar yadda majiyar rahoton ta bayyana, Ratty dai ya riga mu gidan gaskiya a safiyar ranar Larabar da ta gabata bayan ya shafe kwanaki uku a gadon asibiti ba tare da farfadowa ba.

KARANTA KUMA: Yajin Aikin Ma'aikatan Lafiya: Wani Dattijo 'Dan Shekara 50 ya Kashe Kansa a jihar Oyo

Legit.ng ta fahimci cewa, irin shan wuce kima da Ratty ya yiwa muggan kwayun ya sanya suka ci karo da wasu muhimman sassan jikin sa ta yadda ba za su iya ci gaba da amfani ba da hakan ya sanya rai ya yi masa halin sa.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Ministan lafiya na kasa Farfesa Isaac Adewole, ya bayar a umarni ga hukumomin kula da kwayoyin magani da masu yaki da fataucin muggan kwayoyin akan su hana shigo da maganin nan mai sunan Codeine cikin kasar Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel