An tsige ‘dan Sule Lamido daga sarautar Bamaina, jihar Jigawa

An tsige ‘dan Sule Lamido daga sarautar Bamaina, jihar Jigawa

Masarautar Dutse ta sanar da tsige Dakacin Bamaina Mustapha Lamido daga kujerar sarautar Kauyen.

Mustapha Lamido ya kasance daya daga cikin ‘ya’yan tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido.

Sakataren masarautar, Amadu Malami ne ya bayar da sanarwan sannan kuma ya kara da cewa masarautar za ta nada sabon sarki a Bamaina nan ba da bata lokaci ba.

An tsige ‘dan Sule Lamido daga sarautar Bamaina, jihar Jigawa
An tsige ‘dan Sule Lamido daga sarautar Bamaina, jihar Jigawa

Masarautar ta ce ta dauki wannan mataki ne ganin cewa shi wananan sarki na Bamaina wato, Mustapha Lamido ya saka kansa cikin harkar siyasa a jihar sannan kuma da badakalar handame wasu kudade da ake tuhumar sa da mahaifin sa sun handame lokacin da mahaifinsa ke mulkin jihar, cewa har yanzu gabadayan su na fuskantar tambayoyi daga hukumar EFCC.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar shugaban kasa ya shawarci mata da karda su yarda su tara da mazajensu idan har basu da katin zabe

A halin da ake ciki, Sule Lamido na daya daga cikin masu neman kujerar shugabancin ksara Najeriya karkashin leman PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel