Buhari ya kulla wata cinikayya da gwamnatin Kasar China da zata rugurguza darajan Dalan Amurka

Buhari ya kulla wata cinikayya da gwamnatin Kasar China da zata rugurguza darajan Dalan Amurka

Babban bankin kasar China ta sanar da kulla wata alakar cinikayya da Najeriya da zata baiwa kasashen biyu damar musayar kudadensu da nufin samar da Canji ga yan kasuwa da nufin habbaka kasuwanci da kuma rage neman darajar Dala da yan kasuwa ke yi.

Yarjejeniyar da aka kullata a ranar Ahamis 3 ga watan Afrilu ta kunshi musayar kudin China, Yuan biliyan 15, kimanin dalan Amurak biliyan 2.35 kenan, a tsakanin kasashen Najeriya da China cikin shekaru uku, bugu da kari za’a iya kara adadin kudin tare da tsawaita lokacin, idan har kasashen biyu sun amince.

KU KARANTA: Hauwa Maina ta rasu, karanta wasu muhimman bayanai game da ita guda 8 da baka sani ba

Babban bankin kasar China ya bayyana a shafinta na yanar gizo cewa an kulla wannan yarjejeniya ne da nufin daidaita darajan kudaden kasashen biyu da habbaka cinikayya a tsakaninsu, inji rahoton Legit.ng.

Buhari ya kulla wata cinikayya da gwamnatin Kasar China da zata rugurguza darajan Dalan Amurka
Gwamnan Babban Bankin Najeriya da na China

Wannan mataki da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauka ya dace da manufarta na karua darajan Naira, da wannan, yan kasuwa dake shigo da kaya daga China basu bukatar karbar canjin dala, sai dai su karbi canjin Yuan daga babban bankin Najeriya, kai tsaye su sayi kaya daga kasar China, hakan zai rage ma Dala daraja.

Idan za’a tuna a shekarar 2014 ne babban bankin Najeriya ta sanar da yiwuwar karin kudin kasar China, Yuan a baitil Malinta daga matsayin kasha biyu, zuwa kasha bakwai, inda a wannan lokaci dala ya keda kasha 85 na kudaden baitil Malin Najeriya.

Tun a shekarar 2014 ne kasuwannin Duniya suka amince da Yuan a matsayin kudin da za’a iya amfani da shi a ko ina, wannan ya sanya kasashe kamar su Ghana, Afirka ta kudu da Zimbabwe fara amfani da shi, a yanzu ma Najeriya ta dauki gabaran bin sawunsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng