Kiristoci suyi azumin kwanaki 200 sakamakon kisan da akeyi a kasar nan – Babban limami

Kiristoci suyi azumin kwanaki 200 sakamakon kisan da akeyi a kasar nan – Babban limami

- Rev. Uma Ukpai yace hanyar da ita kadai ce mafita ga kisan da filani ke yiwa kiristoci wadanda ke bangaren arewacin Najeriya itace suyi azumi na kwanaki 200 suyi addu’ar kariya

- Ukpai wanda shine ya kirkiro kungiyar Evangalis yace duk matasan da suka wuce shekaru 25 sun gurbata da rashawa saboda haka su fita daga tinanin shiga harkar siyasa

- Ukpai yace bai kamata a ringa daukar kiristoci kamar basu da yawa a kasar nan duk da gagarumar gudunmuwar da suke bayarwa ga ginin kasar da cigabanta

Rev. Uma Ukpai yace hanyar da ita kadai ce mafita ga kisan da filani ke yiwa kiristoci wadanda ke bangaren arewacin Najeriya itace suyi azumi na kwanaki 200 suyi addu’ar kariya.

Ukpai wanda shine ya kirkiro kungiyar Evangalis yace duk matasan da suka wuce shekaru 25 sun gurbata da rashawa saboda haka su fita daga tinanin shiga harkar siyasa a Najeriya.

Ukpai yace bai kamata a ringa daukar kiristoci kamar basu da yawa a kasar nan duk da gagarumar gudunmuwar da suke bayarwa ga ginin kasar da cigabanta, ya fadi hakan ne a garin Uyo, jihar Akwa Ibom lokacin da yake zantawa da jami’in labarai na Nigerian Union of Journalist (NUJ) a jiya.

Kiristoci suyi azumin kwanaki 200 sakamakon kisan da akeyi a kasar nan – Babban limami
Kiristoci suyi azumin kwanaki 200 sakamakon kisan da akeyi a kasar nan – Babban limami

Yayi nadama game da yanda akafi daukar shanuwa da muhimmanci fiye da rayuwar kirista a wasu bangarorin kasar nan, ya kumayi kira ga jami’an tsaro da su dauki mataki na adalci game da yanda filani ke kashe kiristoci wasu bangarorin na kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a harin da aka kai a masallacin Najeriya ya kai 86

Yace kada Najeriya ta tsammaci abun kirki lokaci zabe mai zuwa saboda “Shuwagabannin da zasu karbi mulki suma cikin rashawa zasu shigo saboda gaba daya gwamnatin ta baci da rashawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

KU KARANTA KUMA:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng