Sanata Dino Melaye na nan lafiya a karkashin kulawar tsaro – Yan sanda

Sanata Dino Melaye na nan lafiya a karkashin kulawar tsaro – Yan sanda

Kakakin rundunar yan sandan Najeriya, ACP Jimoh Moshood yace Sanata Dino Melaye na nan lafiya a hannun ya yan sanda.

Kakakin yan sandan ya bayyana hakan lokacin da majiyarmu ta Daily Trust ta kira shi domin tabbatar da sake kamun Sanata Dino Melaye bayan an gurfanar da shi gaban kotu a ranar Laraba.

Yayi bayanin cewa an gurfanar da Dino a kotu ne bisa tuhumar cewa yayi yunkurin gudu daga hannun hukumar tsaro da kuma yunkurin kashe kansa inda aka bayar da belinsa.

Sanata Dino Melaye na nan lafiya a karkashin kulawar tsaro – Yan sanda
Sanata Dino Melaye na nan lafiya a karkashin kulawar tsaro – Yan sanda

Sai dai, Moshood yace har yanzu Sanatan na a hannun yan sanda bisa zargin hada kai wajen tafiyar da bindigogi, fashi da makami da kuma sace mutane wanda ke gaban wata babban kotu dake Lokoja, jihar Kogi.

KU KARANTA KUMA: Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a harin da aka kai a masallacin Najeriya ya kai 86

Ya kuma bayyana cewa ikirarin da akeyi na cewa rayuwar Sanatan na cikin hatsari ba yi bane domin yana a hannun tsaro na yan sanda.

A baya munji yadda Sanata Dino ya duro daga motan yan sanda a kokarinsa na tserewa daga hannunsu inda hakan ya kai shi ga kwanciya a asibiti.

dan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel