Rikicin Boko Haram: shugaban Kiristocin Najeriya ya yi kira da a daina aibanta Shekau da Albarnawi
Tsohon shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, reshen jihar Borno, Rabaran Fada Titus Bona yace cigaba da aibanta shuwagabannin bangarorin Boko Haram guda biyu, Abubakar Shekau da Abu Mus’ab Albarnawi ba zai haifar da da mai ido ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Pona yana cewa zagin shuwagabannin ba zai hanzarta sako yan matan Chibok da dalibar kwalejin Dapchi, Leah Sharibu daga hannun kungiyar yan ta’addan ba.
KU KARANTA: yan bangan siyasa sun kai ma wani na hannun daman gwamnan jihar Kebbi farmaki
Faston ya bayyana hake ne a wani taron addu’ar sakon yan matacn Chibok da daliba Leah da kungiyar dalibai yan asalin kabilar Kibaku suka shirya a ranar Laraba 2 ga watan Mayu a garin Maiduguri.
“Muna addu’a ga shuwagabannin Boko Haram ne saboda su ma iyaye ne, kuma suna da yara da mata, don haka sun san darajar yara da mata, don haka ba sai mun yi ta zagin Shekau ko Albarnawi ba wai don yaranmu na hannunsu ba, abinda ya kamace mu shi ne mu rokesu har su sako mana yayanmu.” Inji shi.
Faston ya bayyana cewa suna iya kokarinsu wajen yin addu’ar Allah ya kubutar da duk mutanen da yan Boko Haram suka yi garkuwa dasu a sakamakon rikicin da ake fama da shi tun daga shekarar 2009.
A nasa jawabin, shugaban al’ummar Musulmai yan kabilar Kibaku ALhaji Yahaya ya bayyana cewa Allah ne ya halicce mu kabilu daban daban, kasashe daban daban da kuma kalar fata daban daban don mu fahimci juna.
“Na yi farin ciki da har muka tsallake batun bambamce bambamcen addini, muka hada kai domin kokarin ceto yayanmu mata da aka sace ba tare da la’akari da wanda zai bada gudunmuwa wajen samun biyan bukatar ba, wannan ya nuna cewa babu wanda zai iya raba Musulai da Kiristocin Chibok da sunan addini.” Inji shi
Daga karshe shugaban kungiyar daliban, Musa Ibrahim Aji ya bayyana godiyarsa ga duk mutanen dake da hannu cikin sako yan matan Chibok 103 da yan ta’addan Boko Haram suka yi a shekarar data gabata, tare da daukan nauyin karatunsu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng