Rashin girmamawar da shugaban ‘Yan Sanda ke nunawa majalisa ba sabon abu bane tunda yayiwa Buhari ma - Saraki
- Shugaban majalisa Bukola Saraki ya nuna rashin jin dadinsa game da shawarar da IG Ibrahim Idris yayi na kin amsa gayyatar majalisar har sau biyu
- A karo na biyu kenan Ibrahim Idris, na kin bayyana a gaban majalisa duk da sakon gayyatar data aika masa
- Majalisar ta gayyace shi ne domin ya amsa mata tambayoyi akan kamawar da hukumar tayiwa sanata Melaye da kuma kisan da ake tayi a fadin kasar
Shugaban majalisa Bukola Saraki ya nuna rashin jin dadinsa game da shawarar da IG Ibrahim Idris yayi na kin amsa gayyatar majalisar har sau biyu.
A karo na biyu kenan Ibrahim Idris, na kin bayyana a gaban majalisa duk da sakon gayyatar data aika masa kamar yanda doka ta amince.
Majalisar ta gayyace shi ne domin ya amsa mata tambayoyi akan kamawar da hukumar tayiwa sanata Melaye da kuma kisan da ake tayi a fadin kasar.
Shugaban hukumar ‘Yan Sandan an gayyaceshi karo na farko ne a ranar Laraba, 15 ga watan Afirilu, amma yaki bayyana a gaban majalisar.
KU KARANTA KUMA: Harin masallacin Mubi: Za mu tsaurara matakan tsaro - Osinbajo
Ya kara da cewa babu wani shugaban hukumar ‘Yan Sanda da majalisar ta taba gayyata yaki bayyana a gabanta.
Shugaban majalisar Bukola Saraki, ya shawarci abokan aikinsa dasu karawa shugaban ‘Yan Sandan wa’adin sati daya ya bayyana a gabanta.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng