Dasuki: Za'a koma kotu cikin makon gobe kan kudaden makamai
- Za a gurfanar da Dasuki da wasu a gaban kotu a ranar 16 ga watan Mayu akan tuhumar su da akeyi da almundahanar kudi
- Za a gurfanar da Col. Sambo Dasuki mai ritaya da wasu mutane hudu a ranar 16 ga watan Mayu, a babbar kotun birnin tarayya dake Maitama, akan zargin 32 da hukumar yaki da rashawa take musu
- Dasuki, tsohon mai bada shawara akan harkar tsaro a karkashin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan an fara gurfanar dashi a watan Nuwamba, 2015

An gurfanar dashi tare da tsohon shugaban fannin kudi da mulki, karkashin ofishin tsohon mai bada shawara akan harkokin tsaro, Shu'aibu Salisu ;tsohon manajan matatar man fetur ta kasa, Aminu Baba-kusa, da kuwa masana'antu biyu- Acacia Holdings da Reliance Referral Hospital.
Hukumar yaki da rashawa ta gurfanar dasu ne da zargin laifuka 19,cin amana da almundahanar kudi Naira biliyan 13.5.
A cigaban sauraron shari'ar ranar laraba, lauyan hukumar yaki da rashawa, Mista Rotimi Jacobs (SAN), ya sanar da cewa sun maida laifukan daga 19 zuwa 32.
Yace gyaran laifukan ya biyo bayan cire Shu'aibu Salisu daga cikin wadanda ake zargi, ya kuma roki kotun da ta karbi gyaran sannan tasa sabuwar ranar sauraron karar.
Lauyan Dasuki, Mista Ahmed Raji(SAN) ya maida martani da cewa kotun ranar 30 ga Afirilu aka yi zaman karshe, kuma sai 1 ga watan Mayu aka sanar dashi.
DUBA WANNAN: Sojin Amurka a Najeriya?
"Ban samu damar zantawa da wanda ake zargi na farko ba kuma an ninka laifuka, gaskiya muna rokon a dage sauraron karar."
Mista Solomon Umoh (SAN), lauyan Kusa da sauran sun roki dage sauraron karar.
Mai shari'a Hussein Baba-yusuf ya amince da ninka zargin da kuma dage sauraron karar zuwa 16 ga watan Mayu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng