Mata a kasar Iran sun canza kama don su shiga filin wasanni suyi kallon wasan kwallon kafa

Mata a kasar Iran sun canza kama don su shiga filin wasanni suyi kallon wasan kwallon kafa

- An kama mata da dama a kasar Iran sun ja hankalin jama’a ta hanyar abubuwan da zasu iyayi domin su shiga filin wasanni su kalli wasan kwallon kafa

- Sun sanya gemu na karya da hular gashi irin na maza domin su batar da kama su samu shiga filin wasanni na Azadi suyi kallon wasan kwallon kafa

- Duk da cewa babu wata doka data hana mata zuwa wurin wasanni a kasar ta Iran koda sunje ma ba’a barinsu shiga, tun al’adar lokacin zuwan musulunci ya bawa mata damar zuwa kallon wasanni

An kama mata da dama a kasar Iran sun ja hankalin jama’a ta hanyar abubuwan da zasu iyayi domin su shiga filin wasanni su kalli was an kwallon kafa.

Sun sanya gemu na karya da hular gashi irin na maza domin su batar da kama su samu shiga filin wasanni na Azadi dake garin Tehran, suyi kallon wasan kwallon kafa, a Juma’ar data gabata.

Duk da cewa babu wata doka data hana mata zuwa wurin wasanni a kasar ta Iran, koda sunje ma ba’a barinsu shiga, tun al’adar lokacin zuwan musulunci a shekarar 1979, da ya bawa mata damar zuwa kallon wasanni.

Mata a kasar Iran sun canza kama don su shiga filin wasanni suyi kallon wasan kwallon kafa
Mata a kasar Iran sun canza kama don su shiga filin wasanni suyi kallon wasan kwallon kafa

A lokacin baya ana hukunta mata idan sukaje kallon wasanni. A shekarar 2014, an daure mai kare hakkin da adam British-Iranian Ghoncheh Ghavami a yunkurin da tayi na zuwa kallon wasan kallon hannu ta maza a kasar Iran.

KU KARANTA KUMA: Manyan kurakurai 5 da maza ke tafkawa wajen neman aure

Sannan a watan Maris, 2018, mata 35 aka daure sakamakon yunkurin shiga filin wan kwallon kafa.

A watan Fabrairu kuma an bar mata sun shiga kallon was an kwallon hannu na maza a Tehran, amma dai sun zauna wuri daban da na maza.

A bangaren kasar Saudiyya kuwa ana nan ana cigaba da kawo sauye-sauye wajen al'addunsu ta yadda zai yi daidai da zamani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel