Harin masallacin Mubi: Za mu tsaurara matakan tsaro - Osinbajo
Gwamnatin Najeriya ta umurci jami'an tsaron kasar da su tsaurara matakan tsaro a kasuwanni da sauran wuraren ibada a garin Mubi dake jihar Adamawa.
Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai wani masallaci da ke kasuwar garin.
Harin dai ya kashe akalla mutum 24 tare da jikkata wasu da dama.
Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bada wsaannan umurnin.
Ya kuma umarci hukumar agajin gaggawa ta kasa wato NEMA da ta gaggauta samar da magunguna da sauran kayayyakin agaji ga wadanda abun ya cika dasu.
Wata sanarwa da kakakin mataimakin shugaban kasar Laolu Akande ya aikewa manema labaru ta ce, Farfesa Osinbajo ya kuma yi ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu.
KU KARANTA KUMA: Ramadan: Malami ya gargadi ‘yan kasuwa game da kara kudin kayayyaki
Osinbajo ya kuma nanata cewar jami'an tsaro na kokarin gano tare da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
Kawo yanzu dai babu wata kungiyar da ta dau alhakin kai wannan harin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng