Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya ya watsawa Sanatoci kasa a ido
- Sufeta Janar na ‘Yan Sanda ya ki karba goron gayyatar Majalisa
- Wannan karo dai ma IGP ya ki bayyana a gaban Sanatocin kasar
- Ibrahim Idris ya aiki wani Mataimakin sa ya wakilce sa a zaman
Labarin da mu ke samu yanzu haka shi ne Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya watau Ibrahim Kpotum Idris ya ki amsa kiran da Majalisar Dattawa tayi masa a yau wanda ba shi bane karon farko.
An shiya cewa yau Laraba ne Shugaban Jami’an ‘Yan Sanda Ibrahim Kpotum Idris zai bayyana gaban Majalisar Dattawa domin yi mata bayani game da abin da ya faru da daya daga cikin Sanatocin kasar watau Dino Melaye.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bada umarni a dauki sababbin Jami’an ‘Yan Sanda 6000
Sai dai bayan an kintsa tsaf ana jiran Sufetan ‘Yan Sandan ya hallara gaban Majalaisa sai aka ji labari cewa bai zo ba. A makon jiya an nemi IG din ya bayyana amma ya kawo uzurin cewa ya tafi wani aiki na musamman a Bauchi.
Kakakin Shugaban ‘Yan Sandan na Najeruta watau ACP Jimoh Mashood ya bayyana cewa dokar kasa ta bada damar Sufeta Janar ya aika wani daga cikin manyan Mataimakan sa ya wakilce sa a irin wannan don haka aka tura wani.
Labari na zuwa mana cewa yanzu haka Sufetan ‘Yan Sandan kasar Ibrahim Idris ya nemi Mataimakin Sufeta da ke lura da harkokin Jami'an kasar DIG Habila Joshak ya amsa kiran Majalisa a madadin sa. Majalisar dai ba tace uffan ba tukun.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng