Rikicin Makiyaya: Mutanen da aka kashe a Zamfara sunfi wadanda aka kashe a Benue da Taraba baki daya - Buhari

Rikicin Makiyaya: Mutanen da aka kashe a Zamfara sunfi wadanda aka kashe a Benue da Taraba baki daya - Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya sake maimaita jawabinsa game da kisan da akeyi a kasar nan a rikicin dake gudana wanda keda alaka da makiyaya

- Lokacin da Buhari ya kai ziyarar gaisuwa a jihar Taraba a ranar 5 ga watan Mayu, ya bayyanawa mutane a garin Jalingo, cewa mutanen da aka kashe a Zamfara sunfi wadanda aka kashe a Taraba da Binuwai

- Jam’iyyar adawa ta PDP ta hau kan shugaban kasar game da jawabinsa, inda suka bayyana jawabin a matsayin rarrabuwar kawuna da rashin tinani

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake maimaita jawabinsa game da kisan da akeyi a kasar nan a rikicin dake gudana wanda keda alaka da makiyaya.

Lokacin da Buhari ya kai ziyarar gaisuwa a jihar Taraba a ranar 5 ga watan Maris, ya bayyanawa mutane a garin Jalingo, cewa mutanen da aka kashe a Zamfara sunfi wadanda aka kashe a Taraba da Binuwai.

Jawabin shugaban kasar ya kawo kace nace a tsakanin al’ummar kasar, inda wasu ke cewa banda ma ba daidai bane jawabin nasa da yayi, kuma ya kara rura wutar zargi game da jawaban da yakeyi.

Jam’iyyar adawa ta PDP ta hau kan shugaban kasar game da jawabinsa, inda suka bayyana jawabin a matsayin rarrabuwar kawuna da rashin tinani.

Rikicin Makiyaya: Mutanen da aka kashe a Zamfara sunfi wadanda aka kashe a Benue da Taraba baki daya - Buhari
Rikicin Makiyaya: Mutanen da aka kashe a Zamfara sunfi wadanda aka kashe a Benue da Taraba baki daya - Buhari

Buhari baiyi wani bayani ba game da jawabin nasa tun a lokacin, sai dai kuma ya kara maimaita jawabin lokacin da ya kai ziyara kasar Amurka.

KU KARANTA KUMA: Trump zai turo da manoman kasar Amurka zuwa Najeriya

Shugaban kasar yace wadanda ke aikata kisan an tsammani an daukosu ne daga wasu kasashe da makaman da suke shigowa dasu ana tsammanin daga kasar Libya ake shigowa dasu dan kawo rikici cikin Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng