Tsaraba 5 da shugaba Buhari ya dawowa yan Najeriya da su daga Amurka
Ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai kasar Amurka ta haifar da yaya masu idanu.
Domin a yanzu haka yayi nasarar kawowa kasar Najeriya abubuwan cigaba wanda zai habbaka tattalin arzikinta dama darajarta a idanun duniya.
Hakan yasa muka yi amfani da damar ziyarar tasa domin kawo maku wasu daga cikin manyan nasarori da shugaban ya dawo dasu daga kasar Amurka.
Gasu kamar haka:
1. Kamfanin sarrafa Abinci na " Burger King Food" da ke Amurka zai zuba jari a Najeriya kan harkar kiwon Kaji.
2. Kamfanin " Heinz Tomatoes" zai hada hannu da manoman Timatir a Najeriya don rubanya adadin timatir da suke samarwa.
3. Kamfanin yin tarakta ta noma, " John Deer" zai kafa reshinsa a Najeriya inda zai fara hada tarakta har 10,000 a cikin shekaru hudu.
4. Wani kamfanin cinikin amfanin Gona na kasa da kasa na Amurka zai sauwaka manoman Najeriya hanyar da za su rika sayar da amfanin gonarsu a kasuwannin duniya.
5. Sai kuma sama da dala milyan 500 da gwamnatin Amurka ta kwato daga hannun barayin gwamnatin Najeriya wadanda za a damkawa kasar kudaden.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya aikawa matasan Najeriya da muhimmin sako, ya masu alkawari
6. Daga karshe manyan kamfanonin Amurka wadanda suka hada da "General Electric", "Chevron, " Proctor, Gamble" da "Boeing aircraft manufacturers" sun yabawa gwamnatin Buhari kan yadda ta samar da zaman lafiya a yankin Niger Delta tare da sauwaka hanyoyin yin kasuwanci a kasar.
A baya Legit.ng ta rwaito cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya aikowa matasan Najeriya da sako, inda ya bukacesu dasu koma harkar noma saboda nan ne inda kasar ta dosa.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kamfaninnika shida na ayyukan gona a kasar Amruka, a ranar Litinin 30 ga watan Afirilu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng