Shugaba Buhari ya yiwa tsaffin shugabannin Najeriya Allah ya isa
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a wata tattaunawa da yayi da gidan yada labarai na Muryar Amurka ya dora alhakin tabarbarewar harkoki a kasar Najeriya kacokam a kan tsaffin shugabannin kasar.
Haka zalika shigaban ya kuma kara yin haske game da kalaman sa akan matasa da suka yi ta jawo cece-kuce kimanin makwonni biyu da suka shude inda yace 'yan jarida ne suka jirkita maganar ta sa.
KU KARANTA: An kama dan tsohon gwamna da laifin badakalar Naira miliyan 40
Legit.ng ta samu cewa haka zalika shugaban ya nuna cewa Allah ne kawai zai sakawa 'yan Najeriya tsakanin su da tsaffin shugabannin ta musamman ma idan aka yi la'akari da yadda suka yi facaka da dukiyar al'umma a wancan lokacin.
A wani labarin kuma, Hadakar nan ta wasu zaratan 'yan Najeriya da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya assasa da zummar maido da martabar kasar a bisa turba daidaitacciya watau Coalition for Nigeria Movement (CNM) ta yi wa shugaba Buhari wankin babban bargo.
Hadakar ta Coalition for Nigeria Movement dai kamar yadda muka samu ta na maida martani ne ga shugaban kasar game da kalaman sa a yayin wata fira da yayi lokacin ziyarar sa kasar Amurka game da yadda tsaffin shugabannin kasar Najeriya suka lalata kasar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng