Matsalar shaye-shaye ta shafi kowa da kowa a kasar nan - Saraki

Matsalar shaye-shaye ta shafi kowa da kowa a kasar nan - Saraki

- A ranar Talatar nan ne shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya yaba wa BBC Africa akan shirin ta na "Africa Eye" wanda yayi tsokaci akan yaduwar shan miyagun kwayoyi a Najeriya

Matsalar shaye-shaye ta shafi kowa da kowa a kasar nan - Saraki
Matsalar shaye-shaye ta shafi kowa da kowa a kasar nan - Saraki

A ranar Talatar nan ne shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya yaba wa BBC Africa akan shirin ta na "Africa Eye" wanda yayi tsokaci akan yaduwar shan miyagun kwayoyi a Najeriya.

A wani bayani da sakataren yada labarai na Saraki ya fitar, Sanni Onogu, ya bayyana cewar Saraki yace shirin da BBC din suke akan shan miyagun kwayoyin da gaske yana faruwa a Najeriya kuma ya kamata a maida hankali don magance matsalar.

DUBA WANNAN: Karya ne batun cewa wuta ta kama a CBN

"Yaduwar shan miyagun kwayoyi a Najeriya shine dalilin da yasa majalisa tayi taro da masu ruwa da tsaki a kano a watan Disamba."

Shugaban majalisar dattawan yace "Duk da ina aiki akan wannan matsalar watanni kadan da suka wuce, kallon shirin da BBC ta saki ya kara bude min ido 'yan Najeriya zasu gani cewa, idan bamu dau mataki ba, zamu zauna cikin bala'i. Saboda haka ba zamu zuba ido muna jiran komai ya daidaita ba. A yanzu haka, bayan taron da akayi na kano a watan Disamba 2017, mun samo mafita game da miyagun kwayoyi da kuma cibiyoyin kiwon lafiyar kwakwalwa."

"Dokar shan kwayoyi ba bisa ka'ida ba da muke son gabatarwa karkashin Hukumar yaki da sha da kuma safarar miyagun kwayoyi ta Najeriya wato (NDLEA) da kuma hukumar NAFDAC da sauran hukumomin da suka dace."

"Dokokin zasu tabbatar da samun cibiyoyin kiwon lafiya da kuma hana shan miyagun kwayoyin a kowacce jiha, tare da tabbatar da kula da masu matsalar tabin kwakwalwa."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: