Wata kungiya ta bukaci da a tsige gwamna Ganduje

Wata kungiya ta bukaci da a tsige gwamna Ganduje

- Wata kungiya mai suna Hamisu Magaji Foundation dake da Ofishi a Kano, tace gwamnan jihar Kano ya karya ka'idar kashe kudin gwamnati wajen bada aikin gina gada da aka dauko daga kan titin gidan Zoo zuwa na Zaria Road akan kudi naira biliyan hudu da rabi

Wata kungiya ta bukaci da a tsige gwamna Ganduje
Wata kungiya ta bukaci da a tsige gwamna Ganduje

Wata kungiya mai suna Hamisu Magaji Foundation dake da Ofishi a Kano, tace gwamnan jihar Kano ya karya ka'idar kashe kudin gwamnati wajen bada aikin gina gada da aka dauko daga kan titin gidan Zoo zuwa na Zaria Road akan kudi naira biliyan hudu da rabi.

DUBA WANNAN: Trump ya nemi goyon bayan Najeriya don basu bakuncin gasar cin kofin duniya na 2026

Shugaban kungiyar Malam Hamisu Magaji yayi kira da a tsige gwamnan jihar, saboda cewar kwangilar bata cikin kasafin kudin da jihar ta ware a bana. Yau kimanin sati uku kenan da suka wuce da gwamnatin jihar ta Kano karkashin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta bada kwangilar aikin gina gadar, da zummar cewar gadar zata kara kawata birnin na Kano.

Sai dai kuma kungiyar tayi zargin cewa, baya da aringizon kudi da gwamnati tayi na kwangilar an kuma keta ka'idojin kashe kudin gwamnati.

Malam Hamisu yace aikin baya cikin kasafin kudin shekarar 2018 da majalisar dokokin jihar ta Kano ta aminta dashi. A cewar shi sun san an ware naira miliyan 150 ne kawai saboda gyaran hanya. Ya kara da cewar aikin da ake yi a yanzu baya kan tsarin doka, saboda haka aikin bai kamata ba. Yace zasu kai kara kotu domin ta saka a dakatar da aikin ba tare da wani bata lokaci ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel