A shirye muke da mu biya N66,500 a mafi karancin albashi - Dankwambo

A shirye muke da mu biya N66,500 a mafi karancin albashi - Dankwambo

- Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwamboya tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye take data daga albashin ma’aikata zuwa N66,500 da zarar sun gama ganawa da kungiyar NLC

- Charles Yau Iliya mataimakin gwamnan wanda shine ya wakilci gwamnan a wurin taron bukin ranar ma’aikata na shekarar 2018, yace gwamnatinsu bazatayi wata tantama ko jayayya ba na Karin albashin da zarar an samu matsaya da kugiyar NLC

- Ciyaman din kungiyar ta NLC Haruna Kamar, yayi kira ga gwamnatin data biya 10% na kudin kula da lafiyar ma’aikatan jihar na kananan hukumomi da kuma Karin girma ga ma’aikatan da malaman firamare

Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye take data daga albashin ma’aikata zuwa N66,500 da zarar sun gama ganawa da kungiyar NLC.

Charles Yau Iliya mataimakin gwamnan wanda shine ya wakilci gwamnan a wurin taron bukin ranar ma’aikata na shekarar 2018, yace gwamnatinsu bazatayi wata tantama ko jayayya ba na Karin albashin da zarar an samu matsaya da kugiyar NLC, don ci gaban ma’aikatan jihar.

A shirye muke da mu biya N66,500 a mafi karancin albashi - Dankwambo
A shirye muke da mu biya N66,500 a mafi karancin albashi - Dankwambo

Ciyaman din kungiyar ta NLC Haruna Kamar, yayi kira ga gwamnatin data biya 10% na kudin kula da lafiyar ma’aikatan jihar na kananan hukumomi da kuma Karin girma ga ma’aikatan da malaman Firamare.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya kunyata kasar Najeriya a ziyarar da ya kai Amurka - PDP

Kungiyar ta NLC ta kumayi kira ga gwamnatin data kara sakin kudi, don a samu sallamar wadanda suka ajiye aiki a jihar ta Gombe, kamar yanda ta bukaci gwamnatin ta budewa kungiyar kamfanin buga takardu da kuma wurin horo na kisan gobara da kuma Ofishin gudanar da ayyukansu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng