Mutane 24 suka rasa rayukansu sakamakon bam da aka tayar cikin wani masallaci a garin Adamawa – Yan sanda

Mutane 24 suka rasa rayukansu sakamakon bam da aka tayar cikin wani masallaci a garin Adamawa – Yan sanda

- Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da rasa rayukan mutane 24 a garin Mubi dake jihar Adamawa sakamakon bamabamai da aka tayar a cikin masallaci a garin na arewa maso gabashin Najeriya

- An tayar da bamabaman ne lokacin da mutanen ke gabatar da sallar azahar a cikin masallacin

- SP Othman Abubakar mai magana da yawun hukumar 'yan sandan yace bam din na farko ya tashi ne da karfe 1pm na rana, ana cikin kwashe gawarwakin kuma na biyun ya tashi

Hukumar 'yan sanda a jihar Adamawa ta tabbatar da cewa mutane 24 suka rasa rayukansu sakamakon bamabamai da aka tayar a cikin wani masallaci a garin Mubi dake jihar Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya.

Bam din ya tashi ne a lokacin da masallatan ke gabatar da sallar azahar a cikin masallacin na garin Mubi.

SP Othman Abubakar mai magana da yawun hukumar 'yan sandan yace bam na farko ya tashi ne da karfe 1 na rana, bayan nan kuma ana cikin kwashe gawarwakin wadanda suka rasu wani kuma ya kara tashi.

KU KARANTA KUMA: Bayan ganawa da Trump, shugaba Buhari ya bar Washington DC

Wani yaro matashi ne ya tayar da bam din cikin masallacin bayan an idar da sallah, ta hanyar rigar da yake sanye da ita a jikinsa ta bam, yaron wanda bazai wuce shekaru 18 zuwa 19 ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng