Hotunan yadda aka gudanar da murnar Ranar Ma'aikata a garin Ibadan
A yau ne aka gudanar da murnar tuna ranar ma'aikata a kasar nan ta Najeriya wadda ta yi daidai ta 1 ga watan Mayun 2018. An saba gudanar da wannan biki a makamanciyar wannan rana ta kowace shekara kamar yadda wasu kasashe suka dabbaka a fadin duniya.
Gwamnatin tarayya ta bayar da hutu ga ma'aikatan kasar sakamakon wannan rana kamar yadda ta saba a kowace shekara.
A yau jardar Legit.ng ta kawo muku hotunan yadda aka gudanar da bikin tuna wannan rana ta ma'aikata a farfajiyar wasanni ta Lekan Salami dake babban birni na Ibadan a jihar Oyo.
KARANTA KUMA: Hotunan Manyan Kasuwanni 7 a fadin Najeriya
Tarihi dai ya bayyana cewa, Najeriya ta fara bayar da hutun a wannan rana yayin da gwamnatin Kano karkashin jam'iyyar PRP ta kaddamar a shekarar 1980.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta kasar nan ta dauki wannan salo ne na tunawa da bayar da hutu ga ma'aikata a ranar 1 ga watan Mayu na shekarar 1981.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng