Sakin layi: Buhari ya bayyana akasarin matasan Arewa a matsayin jahilai

Sakin layi: Buhari ya bayyana akasarin matasan Arewa a matsayin jahilai

A iya cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake kwatawa, a inda ya bayyana matasan Arewacin Najeriya a matsayin jahilai, a yayin ziyarar da ya kai Amurka, inji rahoton jaridar The Cable.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaba BUhari ya bayyana hakane cikin wata hira da yayi da gidan rediyon muryar Amurka, a lokacin da yayi kokarin karin haske game da batun da yayi a kasar Ingila wanda ta tada kura a tsakanin yan Najeriya, inda yake cewa matasan Najeriya malalata ne, kuma cima zaune.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: An samu tashin bama bamai a garin Mubi

Buhari ya bayyana ma majiyarmu cewa da dama daga cikin matasan Arewacin Najeriya suna da alaka da wasu rukuni guda biyu, kodai sun fice daga makaranta ba tare da kammala karatu ba, ko kuma jahilai ne.

“Kasan yawancin matasan Arewa basa kammala karatu suke daina zuwa makaratan, wasu kuma Jahilai ne,da bad an Allah yasa mun samu damuna mai kyau ba, da lamarin ya ta’azzara sosai, kaga ko da ace matasan nan ma sun fita kasashen waje, ba wani abin kirki suke samu ba, don kuwa kudin suke samu baya iya daukan nauyinsu ma.” Inji Buhari.

Daga karshe ya bayyana kafafen watsa labarun Najeriya tamkar suna yin abinda suke so ne, don haka da gangan suka lalata maganan da yayi, suka juya shi da nufin yi masa batanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel