Magana ya lalace: Uwargida ta sharara ma jami’in Dansanda mari a tsakiyar titi

Magana ya lalace: Uwargida ta sharara ma jami’in Dansanda mari a tsakiyar titi

Wata mata mai suna Faith Michael da ta sharara ma jami’in Dansanda mari ta gamu da fushin Kuliya manta sabo a ranar Litinin 14 ga watan Afrilu, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Wannan lamari mara dadi ya faru ne a ranar 14 ga watan Afrilu, inda Uwargida Faith ta fala ma Dansanda Faith Akori mari bayan ta ga alamun yana neman ya bata mata lokaci a lokacin da ya tare wani dan Achabar da ya dauko ta.

KU KARANTA: Jami’an hukumar Kwastam zasu samu karin albashi mai tsoka nan gaba kadan – Hamid Ali

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dansanda mai shigar da kara, Vincent Osuji ya bayyana ma Kotu adadin tuhume tuhume guda hudu da ake zargin matar da aikatawa, da suka hada da: Cin zarafin jami’an tsaro, hana shi gudanar da aikinsa, wulakanta shi, yi masa barazana, muzanta shi da tozarta shi.

Sai dai wanda ake kara ta bayyana ma Kotun cewar Dansandan ne ya ja ma kansa shan mari, inda tace shi ne ya tare dan Achabar da ya daukota akan adaidai mahadar titi ta CBN, inda kuma ya nemi sai dan Achaban ya ba shi naira 50, hakan ya bata mata rai ta zabga masa Mari.

Bayan sauraron dukkan bangarorin, sai Alkali mai shari’a ya dae sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Mayu, sa’annan ya bada belin madam Faith akan kudi naira N20,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel