Mutane 15 sun nutse cikin ruwa yayin haurawa zuwa Turai ci-rani

Mutane 15 sun nutse cikin ruwa yayin haurawa zuwa Turai ci-rani

Akalla mutane 15 su ka nutse yayin da su ke kokarin tsallakawa Nahiyar Kasar Turai kwanan nan kamar yadda mu ka samu labari. Daga ciki akwai wadanda su ka fito daga Yankin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta dauko labari cewa wasu ‘Yan Afrika da ke kokarin shiga Turai ci-rani sun kife a Yankin Kasar Aljeriya. Wani Jami’in da ke kula da Tekun kasar ya bayyanawa ‘Yan Jaridar Kasar Larabawan wannan abin takaici.

Mutane 15 sun nutse cikin ruwa yayin haurawa zuwa Turai ci-rani
Jirgi ya saba nutsewa a cikin ruwa da bakaken Afrika

Akalla mutane 15 wanda duk ‘Yan Afrika ne su ka sheka lahira bayan jirgin da su ke ciki ya nutse cikin ruwa a Yankin Oran da ke kusa da babban Birnin Kasar Aljeriya. Ennahar TV na kasar Aljeriya ta bayyana wannan a makon jiya.

KU KARANTA: Tsagerun Neja-Delta sun yi wa Gwamnatin Buhari barazana

Ministan harkokin cikin gida na kasar Aljeriya ya bayyana cewa kasar na fama da shigowar masu shekawa Turai ci-rani a boye. Hakan ya sa ana samu cunkosa ga masu zuwa kasar Libya da ke Makwabtaka da Kasar ta Arewacin Afrika.

Idan ba ku manta ba dai kwanakin baya ‘Yan Najeriya da ke shiga Turai sun gamu da bakar wahala a kan hanya. Wasu dai ‘Yan kasar nan da kuma Yammacin Afrika na zuwa Turai domin samun abin Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng