Yansandan Najeriya sun yi caraf da wani Dan daba da ya daɓa ma abokinsa wuƙa
Wani matashi mai suna Ifeanyi Chibuzor ya caka ma abokinsa, Daniel Bruce wuka a sakamakon wani zazzafan musu da suka yi a tsakaninsu akan kudi naira 200, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.
A ranar Litinin 30 ga watan Afrilu ne jami’in Dansanda Dalhatu Zannah ya shigar da karar Ifeanyi, inda aka gurfanar da shi a gaban wata Kotun majistri dake garin Abuja, inda yace:
KU KARANTA: Son zuciya bacin zuciya: Yansanda sun yi caraf da barayin babur 2, daya ya mutu a gudun tsira
“A ranar 24 ga watan Afrilu Ofishin Yansandan Utako ta samu kara daga wani mutumi mai suna Daniel Bruce, inda yace da misalin karfe 9 na safiyar ranar Talata, 24 ga watan Afrilu Ifeanyi ya caka ma Bruce wuka a sakamakon musu akan kudi N200.”
Dansanda mai kara Zannah ya bayyana cewar Ifeanyi yayi amfani da fasashshen kwalba ne wajen caka ma Bruce a hannunsa na hagu, inda Bruce ya samu mummunan rauni, shi kuma Ifeanyi ya ranta ana kare, amma daga bisani aka kama shi.
Bugu da kari Zannah ya shaida ma Kotu cewar Bruce ya kashe naira 10,000 wajen kulawa da raunin daya samu a Asibitin Wuse dake babban birnin tarayya, Abuja.
Bayan sauraron karar, sai Alkalin Kotun Abubakar Sadiq ya yanke ma Ifeanyi hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni biyu, sa’annan ya umarce shi ya biya Bruce kudi naira 5,000, amma wanda ake kara ya nemi afuwan Kotu, inda Alkalin ya ci shi tarar kudi N10,000.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng