Sanata ya matsa game da shawarar tsige Buhari
- Ciyaman na kwamitin majalisa na asusun jama’a , Sanata Mathew Urhoghide na jam’iyyar PDP mai wakiltar jihar Edo, yace yana nan kan bakansa game da zancansa na a tsige Buhari
- Urhoghide ya kawo bukatar cewa ayi amfani da sashe na 143 na tsarin dokar kasa ta shekarar 1999, a zaman da akayi na majalisar a ranar Alhamis
- Matasa sun kaiwa Sanatan hari a filin jirgi na Benin, a jihar Edo, game da shawararsa ta tsige Buhari daga bisa mulki
Ciyaman na kwamitin majalisa na asusun jama’a , Sanata Mathew Urhoghide na jam’iyyar PDP mai wakiltar jihar Edo, yace yana nan kan bakansa game da zancansa na a tsige Buhari.
Urhoghide ya kawo bukatar cewa ayi amfani da sashe na 143 na tsarin dokar kasa ta shekarar 1999, a zaman da akayi na majalisar a ranar Alhamis data gabata.
Matasa sun kaiwa Sanatan hari a filin jirgi na Benin, a jihar Edo, game da shawararsa ta tsige Buhari daga bisa mulki.
Sanatan lokacin da majalisar ke tattaunawa game da cire $496m da shugaban kasar yayi bada izinin majalisar ba don siyo jiragen yaki, yasa ya kawo shawarar tsige shugaban daga kan kujerarsa ta mulki.
KU KARANTA KUMA: Wadanda suka ce kada Buhari ya sake tsayawa takara a zaben 2019 masu sonsa ne – Jigon Arewa
A kafar sadarwa labari ya yadu a jiya cewa, Urhoghide ya canza maganar tasa. Amma a jawabin daya fito a daren jiya kuma ya gardanta rahotanni akan hakan.
A halin yanzu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana Birnin Washington inda zai gana da Shugaban kasar Amurkan Donald Trump a makon nan game da wasu batutuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng