Yadda mayakan Boko Haram ke tatsar kudin haraji daga Jama’an Borno da Yobe

Yadda mayakan Boko Haram ke tatsar kudin haraji daga Jama’an Borno da Yobe

Wani binciken kwakwaf da kamfanin dillancin labaru na Reuters ta gudanar da ya nuna yan ta’addan Boko Haram na tatsar jama’an yankin tafkin Chadi, jihar Borno da Yobe dake zaune a yankunan dake karkashin ikonsu kudaden haraji.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani tsagi na kungiyar Boko Haram, ISWA, na rike da kusan kilomita 160 na fadin kasa dake tsakanin Yobe, Borno da yankin tafkin Chadi, duk a yankin Arewa masi gabashin Najeriya.

KU KARANTA: Yadda wata Budurwa ta yanke mazakutan Saurayinta da almakashi bayan ya fitar da bidiyon kwanciyarsu

Wasu makiyaya dake yankin sun bayyana ma majiyarmu cewar suna biyan mayakan Boko Haram N2,500 a matsayin haraji akan kowanni Sa, da kuma N1,500 akan tumaki, haka zalika yan ta’addan suna da gidajen yankan dabbobi inda ake biyan kudi don a yanka dabba, kuma suna siyar da itace da sauran abubuwa.

Yadda mayakan Boko Haram ke tatsar kudin haraji daga Jama’an Borno da Yobe
Mayakan Boko Haram

“Idan kai makiyaya ne, ko dan kasuwa, basu taba ka, abinda suke so kawai shi ne ka yi musu biyayya, kuma ka bi dokokin da suka gindaya a yankunan da suke mulki, jami’an tsaro kawai suke kashewa.” Inji wani makiyayi.

Sai dai Shelkwatan tsaro na Najeriya bata musanta batun biyan harajin ba, amma ta musanta batun akwai wani yanki da yan ta’adda ke rike da shi, kamar yadda Kaakakin shelkwatar ya bayyana.

“Suna kuntata ma jama’a a duk inda suka same su, ba son abu bane wannan, sun dade suna cin zarafin mutane a duk inda suka hadu dasu, amma hakan bawai yana nufin suna rike da wani yankin Najeriya bane, amma muna daukan matakin shawo kan lamarin.” Inji Kaakaki John Agim.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: