Bazamu taba yin shugaban kasar da ba zai iya zuwa Amurka ba – Lauretta Onochie
Sakamakon suka da wasu yan siyasa ke yawan yi game da yawan ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kaiwa kasar Amurka akai-akai, hadimar shugaban kasar Misis Lauretta Onochie a ranar Lahadi ta bayyana cewa Najeriya bazata taba yin shugaban kasar da ba zai iya zuwa Amurka ba.
Ta kuma bayyana dalilan da yasa Buhari ke zuwa Amurka. A cewarta, Buhari ya je tattauna muhimman batutuwa da zasu kawo ci gaban kasar ne.
Karata jawabinta a kasa:
"Bazamu taba yin shugaban kasa da ba zai iya zuwa kasar Amurka ba.
"Shugaban kasa Buhari ya isa Washington akan ziyarar aiki.
"Barack Obama ya ji dadi a lokacin da ya samu labarin cewa Najeriya tayi fatali da manyan barayin gwamnati.
"Barack Obama da kansa ya yaba ma Buhari cewa yayi gagrumin aiki. A yanzu Buhari na kasar Amurka domin tattauna batutuwa kawo ci gaba tare da shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
"Ya samu tarba daga yan Najeriya dake murnar ganin shugaban kasar su mai kwazon aiki.
"Najeriya bazata taba yin shugaban kasar da ba zai ya zuwa Amurka ba. Gidan majalisar Dinkin Duniya. Akwai yan Najeriya da dama a Amurka fiye da wasu garuruwan kasar ma. Bazamu iya mallakar shugaban kasar da bazasu gani ba. Allah ya kiyaye."
KU KARANTA KUMA: Majalisa ba ta da ikon aikawa Shugaban kasa sammaci -Masana tsarin mulki
Idan ba ku manta ba dai yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana Birnin Washington inda zai gana da Shugaban kasar Amurkan Donald Trump a makon nan game da wasu batutuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng