Zaman kadaici yasa tsofaffi yin sata a kasar Japan

Zaman kadaici yasa tsofaffi yin sata a kasar Japan

- Da niyyar fita daga halin kadaici da yayi wa rayuwarsu katutu, tsofaffi da yawa na cigaba da yin sata a kasar Japan. Dalilin da yasaka yawan masu laifi tsofaffi yake cigaba da karuwa kullu yaumin a kasar ta Japan

Zaman kadaici yasa tsofaffi yin sata a kasar Japan
Zaman kadaici yasa tsofaffi yin sata a kasar Japan

Da niyyar fita daga halin kadaici da yayi wa rayuwarsu katutu, tsofaffi da yawa na cigaba da yin sata a kasar Japan. Dalilin da yasaka yawan masu laifi tsofaffi yake cigaba da karuwa kullu yaumin a kasar ta Japan.

DUBA WANNAN: A bisa dukkan alamu dai Dino Melaye zai samu nasara a kiranyen da ake yi masa

A kasar ta Japan duk tsofaffin da suka fito daga gidan da basu samun kulawa sun gwammaci tafiya gidan kurkuku, saboda sunfi samun kulawa da kuma shiga cikin jama'a a can. Kasar Japan tana daga cikin jerin kasashe na duniya wanda al'ummar su suka fi tsufa, inda kashi 27 cikin dari na al'ummar kasar keda sama da shekaru 65 da haihuwa.

Hasashe ya nuna cewar kusan rabin tsofaffin dake kurkuku, an kama sune da laifin sata.

A wani bincike da aka yi mai zurfi a kasar ta Japan, binciken ya nuna cewar kashi 50 cikin dari na tsofaffin dake gidan kurkuku, sata ce ta kai su kurkukun. Hakazalika kashi 40 daga cikin dari na masu satar mata ne da suke rayuwa cikin kadaici, saboda rashin mai debe musu kewa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel