Sallar Musulmai na maganin cutar baya da gabban jiki inji Masana

Sallar Musulmai na maganin cutar baya da gabban jiki inji Masana

Masana a wata Jami'a a Kasar Amurka sun yi wani bincike inda su ka gano cewa sallar da Musulmai ke yi ta na taimakawa wajen kara lafiyar mutum. Idan dai har ana yi sallar da kyau, za a samu saukin kamuwa da irin su cutar baya.

Jaridar Independent ta Turai kwanaki ta rahoto cewa sallah tana da amfani ga zuciyar ‘Dan Adam, bayan nan kuma tana taimakawa gwiwa da hannuwa. A kowace rana ta Allah dai kusan Musulmai Biliyan 2 ke kallon alkiblar kasa mai tsarki.

Sallar Musulmai na maganin cutar baya da gabban jiki inji Masana
Idan aka yi sallah da kyau jiki na samun lafiya inji kwararru

Musulmai kan yi sallah ne akalla sau 5 a kowane yini inda masana su kace motsin da ake yi ya fi na sauran atisaye irin su Yoga. Wani Masani mai suna Mohammad Khasawneh yana cikin wanda su kayi wannan bincike kuma aka buga a Duniya.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun samu galaba kan ‘Yan ta’adda

Na’urorin zamani sun nuna cewa mikewa da sunkuyawa da ake yi lokacin sallah yana maganin ciwon baya. Haka kuma Sujuda yana kara karfin gabban kafafu kwarai. Wannan Masani dai kwararren ne a wata Jami’ar Pennsylvania ta Kasar Amurka.

A binciken da aka yi, an dai gano cewa ana iya warkar da masu larurar kashi ta hanyar sallah. Yayin da su ka rika yin sallah a kai-a kai za su samu sauki inji wannan Babban Masani Mohammad Khasawneh.

Dazu kuma Legit.ng ta rahoto maku cewa Rundunar Sojojin Najeriya da ke yaki da ‘Yan ta’adda a kasar sun damke wasu mutane har 4 da ake zargi ‘Yan Boko Haram ne a Jihar Yobe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng