Boko Haram: Sojojin Najeriya sun samu galaba kan ‘Yan ta’adda a Yobe
Labari ya kai gare mu cewa Rundunar Sojojin Najeriya da ke yaki da ‘Yan ta’adda a kasar sun damke wasu mutane har 4 da ake zargi ‘Yan Boko Haram ne a wasu Garuruwa a cikin Jihar Yobe.
Wadanda ake zargi da cewa ‘Yan ta’addda ne sun fada hannun Sojojin Operation Lafiya Dole ne a Ranar Juma’ar nan 27 ga Watan Afrilu kamar yadda Darektan yada labarai na gidan Sojin kasar Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayyana.
Janar Texas Chukwu ya bayyana sunayen wadanda aka kama da kuma kayan da aka samu a hannun su. Bataliya ta 223 na Operation LAFIYA DOLE ce dai tayi wannan namijin kokari a Garin Damagun da ke cikin Karamar Hukumar Fune.
KU KARANTA: Wani Matashi yayi barna a Kudancin Najeriya
Ga sunayen wadanda aka kama da adadin shekarun su:
1. Chari Masaa (shekaru 40)
2. Gonbuzu Abar (shekaru 30)
3. Modu Moduchollo (shekaru 20)
4. Titta Masawa (shekaru 20)
Bayan nan kuma an kama wani mai daure-masu gindi mai suna Gambo Idrissa mai shekara 30 a Duniya.
Daga cikin abubuwan da aka samu daga hannun su akwai
1. Wayoyin zamani kirar Techno 4
2. Makudan kudi har N150, 000
Dama kuma kafin nan Sojojin da ke Garin Fatiskum sun kama wani ‘Dan ta’addan mai suna Salisu Musa ‘dan shekara 30 a Kauyen Sabon Gari Duddaye da ke cikin Nangere.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng