An samu Man Fetur da Iskar Gas mai yawa a Arewacin Najeriya

An samu Man Fetur da Iskar Gas mai yawa a Arewacin Najeriya

Wannan dai shine karon farko da kamfanin Man Fetur na kasa wato NNPC dake jagorantar wasu kamfanonin hakar Mai na kasar China a wannan hakilon keyin albishir da samun Man Fetur da Iskar Gas a rijiyoyin gwaji a jihar Bauchi.

An samu Man Fetur da Iskar Gas mai yawa a Arewacin Najeriya
An samu Man Fetur da Iskar Gas mai yawa a Arewacin Najeriya

A ganawa da manema labarai akan kalubalen da kuma inda aiki ya kwana, shugaban kamfanin na NNPC, Engr. Mai Kanti Baru, yace lallai kwalliya ta fara biyan kudin sabulu a wannan hakilon da aka yi watsi dashi a 'yan shekarun baya.

Wannan dai shine karon farko da kamfanin Man Fetur na kasa wato NNPC dake jagorantar wasu kamfanonin hakar Mai na kasar China a wannan hakilon keyin albishir da samun Man Fetur da Iskar Gas a rijiyoyin gwaji a jihar Bauchi.

A ganawa da manema labarai akan kalubalen da kuma inda aiki ya kwana, shugaban kamfanin na NNPC, Engr. Mai Kanti Baru, yace lallai kwalliya ta fara biyan kudin sabulu a wannan hakilon da aka yi watsi dashi a 'yan shekarun baya.

DUBA WANNAN: An samu dai-daito a garin Akure bayan rikicin da aka samu tsakanin Hausawa da Yarabawa

"Muna so mu toni rijiya a yankin Yankari wacce zata kai zurfin kafa dubu ashirin, kuma a wurin an fara samun Man Fetur da kuma Iskar, kuma muna ganin cewar idan aikin harkar yayi zurfi za'a samu alkhairi sosai a wurin," inji shi.

Wannan albishir na NNPC dai yasha banban da ikirarin kamfanin hakar mai na kasa da kasa Shell da Chevron, wadanda bayan gwada kwazon su a wasu rijiyoyin gwaji a shekarar 1964 suka yi watsi da wannan aiki baki dayan sa kan cewar ba fita balle riba.

Sai dai a cewar Dakta Isa Tahir masani kan albarkatun kasa, ya bayyana cewar dama tun farko su sunyi imanin cewar gaskiya zata bayyana.

"Misalin da zan bayar a nan shine a lokacin da aka je neman Mai a kasar Libya, anyi ta faman tona rijiyoyi ba a samu, sai daga baya wani masanin albarkatun kasa na kasar Libyan, yace a tona rijiyar har sai anji an tabo dutse tukunna, hakan kuwa aka yi kuma cikin ikon Allah an samu Mai din, amma dai mu nan muna ganin cewar hakar rijiyar ba sai ya kai hakan bama za'a samu wadataccen Mai, saboda kamar yanda kamfanin NNPC din suke yi mana bayani cewar an inganta na'urorin hakar Man. Domin kuwa maganar da nake yanzu ba wai muna maganar babu mai bane, mai akwai shi, amma muna maganar mai wanda za'a hako a samu riba" inji shi.

A halin da ake ciki dai yanzu al'ummar dake yankin wannan wuri da ake yin gwaji na dajin Yankari suna cike da murna da kuma fatan alkhairi ga kasa baki daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng