Tsananin Kyawun Matar sa: Ya nemi Kotu ta raba auren su

Tsananin Kyawun Matar sa: Ya nemi Kotu ta raba auren su

Wani Magidanci Arnold Masuka mai shekaru 40 a duniya, cikin zubar hawaye ya roki babbar kotun Chireya dake garin Gokwe a kasar Zimbabwe akan ta raba auren su da matar sa sakamakon baiwa ta tsananin kyawu da kuma cikar sura.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Arnold dai yana begen kotun ta raba auren su da matar sa Hilda Mleya mai shekaru 30 a duniya a sakamakon tsananin kyawu da sura da Mai duka ya zuba ma ta.

Tsananin Kyawun Matar sa Ya nemi Kotu ta raba auren su
Tsananin Kyawun Matar sa Ya nemi Kotu ta raba auren su

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan magidanci ya shaidawa kotun ko wadataccen bacci baya iya samu sakamakon kyawun matar sa da a yanzu yake neman su sawwake juna.

Arnold ya ci gaba da cewa, ta kai ta kawo kullum yana cikin fargabar fita aiki kuma ya bar matar sa a gida cikin tsammanin ta iya daukar hankalin wasu mazajen.

KARANTA KUMA: Gayyatar Shugaba Buhari zuwa Fadar White House alama ce ta kyakkyawar dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka - Lai Muhammad

Ya kara da cewa, ba zai iya ci gaba da rayuwa kullum cikin zulumi da kuma fargaba duk da kasancewar su na da 'ya'ya a tsakanin su.

Rahotanni sun bayyana cewa Alkalin Kotun ya shawarce su akan su dau dangana ta ci gaba da zama a matsayin mata da miji, inda Arnold ya nuna rashin amincewar sa tun dai an ce shawar daukan daki kuma gyara kayan ka ba ya zama sauke mu raba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng