A karamci irin na Sarkin Bauchi ya baiwa shugaba Buhari muhimman kyautuka guda biyu (Hotuna)

A karamci irin na Sarkin Bauchi ya baiwa shugaba Buhari muhimman kyautuka guda biyu (Hotuna)

A yayin ziyarar aiki na kwanaki biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar Bauchi, Buharin ya gamu da karamci kwarai da gaske, ta yadda al’ummar jihar Bauchi suka nuna masa so da kauna, kamar yadda suka saba nuna masa tun lokacin da ta shiga siyasa.

Legit.ng ta ruwaito mai martaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwan Sulaiman Adamu ya baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari muhimman kyautuka guda biyu a yayin da ya ziyarci fadarsa a ranar Alhamis 26 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Ci ma zaune cikin Matasa: Kotu ta bulale wani matashi barawon Fanka

A karamci irin na Sarkin Bauchi ya baiwa shugaba Buhari muhimman kyautuka guda biyu (Hotuna)
Sarki na mika ma Buhari Al-Qur'ani

Sarkin ya baiwa shugaba Buhari kyautar Al-Qur’ani, da wasu kima kiman bijiman shanu guda biyu, a matsayin wata alama ta karrama bako, kamar yadda aka san mutannen Bauchi.

A jawabinsa, mai martaba Sarki Rilwan ya yaba ma shugaban kasa tare da jinjina masa, musamman game da yadda yake martaba yan jihar Bauchi, tare da mutuntasu, sa’annan ya gode masa da mukaman da ya baiwa yayan jihar.

A karamci irin na Sarkin Bauchi ya baiwa shugaba Buhari muhimman kyautuka guda biyu (Hotuna)
Shanu

A wani labarin kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare ziyarar aiki na kwanaki biyu da ya kai jihar Bauchi, inda ya sauka fadar gwamnati dake Abuja da misalin karfe 11 na ranar Juma’a, 27 ga watan Afrilu.

Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai shilla kasar Amurka don amsa gayyatar shugaban kasar Amurka, Donald Trump a ranar Litinin 30 ga watan Afrilu.

A karamci irin na Sarkin Bauchi ya baiwa shugaba Buhari muhimman kyautuka guda biyu (Hotuna)
Ziyarar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel