'Yan sanda sun gano wasu makamai masu hadari a wani gari dake iyaka da jihar Kebbi

'Yan sanda sun gano wasu makamai masu hadari a wani gari dake iyaka da jihar Kebbi

- Hukumar 'yan sanda ta jihar Kebbi sun gano makaman ne garin a kaboro, dake da iyaka da jihar Kebbi da kuma jihar zamfara

- Kwamishinan ' yan sandar jihar, Kabiru Ibrahim ya tabbatar wa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar

'Yan sanda sun gano wasu makamai masu hatsari a yankin jihar Kebbi
'Yan sanda sun gano wasu makamai masu hatsari a yankin jihar Kebbi

Hukumar 'yan sanda ta jihar Kebbi sun gano makaman ne garin a kaboro, dake da iyaka da jihar Kebbi da kuma jihar zamfara.

Kwamishinan ' yan sandar jihar, Kabiru Ibrahim ya tabbatar wa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.

DUBA WANNAN: Rikicin Makiyaya: An jiwa Kansila da yaran sa ciwo

Ya bayyana cewa jami'an 'yan sandan sun shiga kauyen inda suka samo makamai wanda suka hada da bindigogi masu kirar AK-47 guda 13, sai kuma wasu mugayen makamai 650 da kuma harsashi marasa lasisi.

Yace an kama mutane bakwai da ake zargin su na da alaka da makaman, yanzu haka ana binciken su, inda aka gano bayan wannan ma sun aikata laifuka da dama wanda ya hada da fashi da makami. Yace da an gama bincike za a mika wadanda ake zargi zuwa kotu don yanke musu hukunci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: