Mun rasa mutane 8 a harin da aka kawo jihar Binuwai - Sarkin hausawan Makurdi
- Mutane takwas ne aka kashe, sai sha daya kuma sun bace, sannan sama da 20 kuma sun samu raunuka a jikinsu, sai shaguna da dama da aka fasa
- Sarkin Hausawan Makurdi Alhaji Bello Sallau Abdurrahman ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace an kai harin a kan hausawa ne
- Abdurrahman yace mutane na cikin tsoro da iyalansu sakamakon harin da matasan Tiv ke kai musu suna kasu babu dalili
Mutane takwas ne aka kashe, sai sha daya kuma sun bace, sannan sama da 20 kuma sun samu raunuka a jikinsu, sai shaguna da dama da aka fasa, sakamakon harin da matasan Tiv suka kaiwa hausawan a birnin Makurdi dake jihar Binuwai.
Sarkin Hausawan Makurdi Alhaji Bello Sallau Abdurrahman ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace an kai harin a kan hausawa ne, ya bayyana hakan ne ga manema labarai na Daily Trust ta wayar salula, a ranar Alhamis bayan sun kirashi daga birnin tarayya.
Abdurrahman yace mutane na cikin tsoro da iyalansu sakamakon harin da matasan Tiv ke kai musu suna kasu babu dalili, yace yana mamakin dalilin da yasa suke yin hakan ba tinda hausawa dai ba sune filanin dake kai hari a jihar ba.
Yayi kira ga gwamnatin tarayya data bawa mutanensa da sukayi asarar dukiyoyinsu diyya da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin.
KU KARANTA KUMA: Kakakin gwamna Tambuwal, Imam Imam ya rasu
A halin da ake ciki, Buhari ya gargadi mutanen jihar Benuwe da kada su yarda wasu tsirarun mutane su dinga hada su fada saboda wata bukata tasu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e
Asali: Legit.ng