Rikicin Makiyaya: An jiwa Kansila da yaran sa ciwo

Rikicin Makiyaya: An jiwa Kansila da yaran sa ciwo

- A wani rikici da aka samu tsakanin makiyaya da manoma a garin kansilan da yake wakiltar garin na Gawu dake karamar hukumar Abaji, Suleiman Ibrahim, da kuma wasu mutane biyu sunji mummunan raunuka. Mutanen biyun wanda aka bayyana su da Mahmuda Abubakar da kuma Kabiru Suleiman, sun samu raunuka sanadiyyar saran su da aka yi da adda a ranar Alhamis dinnan

Rikicin Makiyaya: An jiwa Kansila da yaran sa ciwo
Rikicin Makiyaya: An jiwa Kansila da yaran sa ciwo

A wani rikici da aka samu tsakanin makiyaya da manoma a garin kansilan da yake wakiltar garin na Gawu dake karamar hukumar Abaji, Suleiman Ibrahim, da kuma wasu mutane biyu sunji mummunan raunuka. Mutanen biyun wanda aka bayyana su da Mahmuda Abubakar da kuma Kabiru Suleiman, sun samu raunuka sanadiyyar saran su da aka yi da adda a ranar Alhamis dinnan.

DUBA WANNAN: Buhari ya gargadi mutanen jihar Benuwe kada su bari wasu suyi amfani dasu su raba kansu

Wani shaida wanda ya bayyana sunan sa da Yahaya, yace rikicin ya samo asali ne a dai dai lokacin da wasu makiyaya suka shiga da shanun su gonar kansilan da misalin karfe 11 na safe, inda suka bata gyaran da aka yi a gonar domin yin noma. Yahaya yace hakan da makiyayan suka yi ya bata wa wasu samari rai wadanda suka rako kansilan gonar. Inda suka yi zargin cewar makiyayan sun ciri doya da aka shuka a gonar.

"A lokacin da abin ya faru nima ina cikin gona ta, sai naji suna zage-zage da junan su, wani daga cikin samarin da suka rako kansilan yayi kokarin ya kwace saniya daya daga wurin makiyayan, inda shi su kuma makiyayan suka nuna hakan ba zai yiwu ba, a take suka farwa kansilan da matasan nashi."

Ya ce kansilan da mutanen nashi anyi maza an garzaya dasu wani asibiti mafi kusa dake kauyen Mawogi, inda ya bayyana cewar daga baya manya suka shiga maganar, abinda ya zuba wa rigimar ruwa kenan.

Da aka tuntubi, ofishin 'yan sanda na Gwagwalada, ACP Mijinyawa Jahun, ya tabbatar da afkuwar lamarin. Inda yace an kai shari'ar gaban sarkin Abaji, Alhaji Adamu Baba Yunusa, inda ya umarci duka wanda suke da hannu a rikicin su bayyana a gaban shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng