Jam'iyyar PDP reshen jihar Kano tayi taron 'yan takarar gwamna

Jam'iyyar PDP reshen jihar Kano tayi taron 'yan takarar gwamna

- Jam'iyyar PDP a kano tayi kira ga 'yan takarar gwamnan a karkashin inuwar jam'iyyar dasu bi kundin tsarin siyasar jam'iyyar.

- Shugaban jam'iyyar na jihar Senator Mas' up El-Jibril Doguwa ya tattauna da manema labarai jim kadan da gama taron da sukayi na wayar da kan 'yan takara akan kamfen din zaben 2019

Jam'iyyar PDP reshen jihar Kano tayi taron 'yan takarar gwamna
Jam'iyyar PDP reshen jihar Kano tayi taron 'yan takarar gwamna

Jam'iyyar PDP a kano tayi kira ga 'yan takarar gwamnan a karkashin inuwar jam'iyyar dasu bi kundin tsarin siyasar jam'iyyar.

Shugaban jam'iyyar na jihar Senator Mas' up El-Jibril Doguwa ya tattauna da manema labarai jim kadan da gama taron da sukayi na wayar da kan 'yan takara akan kamfen din zaben 2019.

DUBA WANNAN: An kashe Hausawa da yawa a jihar Benuwe

Majiyar mu Legit.ng ta lura da cewa,' yan takarar da suka samu halartar taron sun hada da Alhaji Salihu Sagir Takai, Dr Umar Musa Mustapha (Mai Mustalata), Engr Bello Sani Gwarzo, Alhaji Mamuda Sani Madakin Gini, Alhaji Garba Yusuf, Alhaji Sadiq Aminu Wali, Alhaji Nasiru Madina Fagge, Alhaji Ahmed S Aruwa, Engr Sarki Labaran da Alhaji Nasiru Muhammad.

Doguwa yace Damokaradiyya ta yarda da bawa 'yan takara damar fitowa don jama'a su sansu.

"Mun sanar da ' yan takarar gwamnan jiha yanda zasuyi amfani da taro da shafukan zumunta a lokacin kamfen dinsu don gujewa hada fada a tsakanin mambobin jam'iyyar," yace.

Ya kuma ce 'yan takarar gwamnan mutane 12 da suka halarci taron sun jajanta matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta a jihar. Inda jam'iyyar ta horesu da su kawo tasu gudummawar don magance matsalolin.

" Mun kuma fada musu cewa jam'iyyar ce a gaba don haka ba wanda zai zauna kara zube. Jam'iyyar zata cigaba da kula da al'amuransu. Duk kuma wanda aka tsayar a matsayin 'dan takara dole ne yabi dokokin jam'iyyar a duk al' amuranshi na siyasa."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: