Buhari ya tsallake rijiya da baya, yayinda wasu Sanatoci suka yi yunkurin tsige shi

Buhari ya tsallake rijiya da baya, yayinda wasu Sanatoci suka yi yunkurin tsige shi

- A wani yunkuri da wasu daga cikin 'yan majalisar dattijai suke yi na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kan kujerar shi, a bisa dalilin su na cewar ya fitar da kudi an sayi jiragen yaki ba tare da ya nemi shawara daga wurin su ba, a yanzu haka dai hakar su bata cimma ruwa ba. Sanatocin sun zargi shugaban kasar da fitar da dala miliyan 496 domin sayo jiragen yaki daga kasar Amurka, ba tare da amincewar majalisar dokoki ba

Buhari ya tsallake rijiya da baya, yayinda wasu Sanatoci suka yi yunkurin tsige shi
Buhari ya tsallake rijiya da baya, yayinda wasu Sanatoci suka yi yunkurin tsige shi

A wani yunkuri da wasu daga cikin 'yan majalisar dattijai suke yi na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kan kujerar shi, a bisa dalilin su na cewar ya fitar da kudi an sayi jiragen yaki ba tare da ya nemi shawara daga wurin su ba, a yanzu haka dai hakar su bata cimma ruwa ba. Sanatocin sun zargi shugaban kasar da fitar da dala miliyan 496 domin sayo jiragen yaki daga kasar Amurka, ba tare da amincewar majalisar dokoki ba.

DUBA WANNAN: A kowacce shekara, kasar nan na asarar N136b ga makwabta saboda tsafta da tsarin gabar ruwansu

Shugaban kasar ya bayyana wa majalisar dokokin cewar ya riga ya bada izinin cire kudin, yayinda a yanzu haka kudin ya riga ya shiga asusun kasar Amurka. A cikin wata wasika da shugaban kasar ya rubuta a ranar 13 ga watan nan, wadda aka karanta a gaban majalisar dattijai, wasikar ta tabbatar da biyan kudin.

Duk da haka dai, 'yan jam'iyyar adawa ta PDP sun ce shugaban kasar ya keta kudin tsarin mulki, kuma sun nemi ayi amfani da sashi na 143 na tsarin mulkin kasar nan domin a tsige shi daga kan mulki. Sanata Mathew Uroghide (PDP, Edo) shine sanata na farko daya fara kira da tsige shugaban kasar. "A cewar shi, dole ne ayi amfani da sashi na 143 na kundin tsarin mulkin kasar nan, domin a gabatar da doka a kanshi, domin kuwa shugaban kasar ya keta dokar lasa," inji shi.

Sanata Uroghide ya samu goyon bayan Sanata Chukwuka Utazi (PDP, Enugu) da Sam Anyanwu (PDP, Imo), wanda suka bukaci a dauki hanyar gabatar da tsige shugaban kasar cikin gaggawa.

Sai dai kuma, Sanata Shehu Sani na jihar Kaduna, yaki bada goyon bayan shi akan tsige shugaban kasar, inda yake cewa, "A nawa ra'ayin ina ganin tsige shugaban kasar bashi da wani fa'ida, kamata yayi mu tursasa shugaban kasar a dawo da kudin."

Domin nuna goyon baya ga kudurin Sanata Shehu Sani, Sanata Abu Ibrahim na jihar Katsina, yace shugaban kasar ya yanke hukuncin sayo makaman ne saboda, abinda ya kamata kasar nan ta saka a gaba kenan, wato magance matsalar tsaro.

Sanata Ibrahim, yace kamata yayi a yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, tunda har ya kawo maganar gaban majalisar dokoki, yace gwamnatocin da suka gabata na Olusegun Obasanjo da Goodluck Ebele Jonathan sunyi wadaka da kudin kasar nan ba tare da neman amincewar majalisar dokoki ba, amma dukkan su babu wanda ya nemi a tsige su, sai shi da yake yi domin cigaban kasa.

"Ina ganin wannan wani makirci ne na jam'iyyar adawa, shugaban kasa yayi namijin kokari da har ya kawo maganar gaban mu, domin kuwa daman rarar kudin danyen mai anyi shi ne, saboda bukata irin wannan."

A nasa jawabin, shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, yace a watan Agustan bara, gwamnatin kasar amurka ta zauna dasu kafin ta amince da sayar da jiragen ga Najeriya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng