Tsaro: Buhari zai gurfana gaban ‘yan Majalisar Wakilai da ta Dattijai don amsa tambayoyi
- A karon farko Majalisa ta sammaci shugaban kasa Buhari kan matsalar tsaro
- A yayin da zai gurfana gaban Majalisar dai zai kasance duk Majalisun kasar ne zasu ritsa shi don yi masa tambayoyi
Majalisar Dattijai ta ta marawa takwararta ta wakilai baya wajen bukatar lallai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a gabanta domin yi musu bayani kan yadda al’amuran tsaro suke kara tabarbarewa a kasar nan.
Wannan sabuwar shawara da Majalisar Dattijan ta yanke na bin sahun majalisar wakilan, ya biyo bayan kudirin da Sanata George Akume yayi na bayyana rashin gamsuwa da yadda ala’amarin tsaron yake sake ta’azzara musamman a jihar ta Benue tun daga watan Janairun 2018.
Akume ya bayyana cewa, duk da wanzuwar Sojoji a jihar, amma hakan bai sa ta sauya zani ba wajen kai hare-haren da yan ta’addan suke yi ba.
KU KARANTA: Majalisa ta bukaci kamfanin sarrafa man fetur na NNPC ta mayarwa gwamnatin tarayya da N216bn na tallafin man fetur tallafin-man-fetur
A yanzu dai duk sanda shugaba Buharin zai gurfana a gaban Majilisar ta wakilai zai kasance suma Majalisar Dattijan suna tare da su don yi masa tambayoyin tare.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng