Yadda zalamar kudi ke janyo turmutsutsun tashar ruwan Lega
- Turmutsutsun ababen hawa da injinan fito yana sanya wa a dau lokaci kafin kaya su fito
- Kusan komai na Najeriya daga gabar ruwan Legas ake hiddo su
- Ana samun yawaitar go-sulo a jihar mai tarin jama'a, ana kuma samun tsaiko a gabar ruwan
Shugaban karamar hukumar Apapa ta jihar Legas, Hon Elijah Adele ya danganta kashi 70 cikin dari na cunkoson da ake samu a titi da maido da kamfanoni masu kwadayin samun ciniki.
Adele ya samu zantawa da sababbin zababbun kungiyar Maritime Reporters Association of Nigeria wanda Mista Anya Njoku yake shugaban ta.
Shugaban karamar hukumar Apapa yace mazauna Apapa sun takura da cunkoson titunan ko a lokacin da yake jajen. Kamar yadda shugaban yace, mafi yawan kamfanonin, kwadayi ne yasa suka ajiye kwantenoni babu komai ciki jere a bakin titi
Adele ya fada ma manema labarai cewa wannan dalilin ne yasa yake so ya kange gurin don hana manyan motoci samun shiga kananan tituna da unguwannin Apapan.
DUBA WANNAN: Zamu saki bincike da muka yi kan kalaman TY Danjuma kowa ya gani
Yace abin danasani ne ace Nigerian Ports Authority (NPA) da ke da alhakin duba kamfanoni masu shigo da kaya ta jirgin ruwa da lasisin su sun gaza yin aikin su.
"Babban kalubalen da manyan motoci ke samu a titunanmu shi ne matsalar da kamfanonin jiragen ruwa ke haddasawa, kashi 70 cikin dari na cunkoson kan titunanmu na Apapa kamfanonin ke jawowa."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng