Muhimman ayyuka guda 6 da Atiku Abubakar ya lashi takobin aiwatarwa idan ya zama shugaban Najeriya

Muhimman ayyuka guda 6 da Atiku Abubakar ya lashi takobin aiwatarwa idan ya zama shugaban Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai mayar da hankali, tare da bada fifiko ga wasu muhimman ayyuka guda shida, 6, da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza akansu idan har ya zama shugaban kasa a shekarar 2019, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Atiku ya bayyana haka ne a cibiyar Chatham House dake birnin Landan, yayin da ya gabatar da wata kasida game da yadda za’a habbaka tattalin arzikin Najeriya ta yadda zai amfani yan kasa ta hanyar samar da ayyukan yi, tsaro da cigaba mai daurewa.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Kotu ta garkame Sanatan Najeriya ya Kurukukun jihar Legas

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Atiku yana cewa idan ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya a zaben 2019, zai tabbatar da hada dukkanin asusun da Najeriya ke ajiyan kudadenta, inda yace asusun kudin rarar mai, asusun kudin ko ta kwana, da asusun kudin tabbatar da daidato na gwamnati, duk hade su waje daya.

Muhimman ayyuka guda 6 da Atiku Abubakar ya lashi takobin aiwatarwa idan ya zama shugaban Najeriya
Atiku Abubakar

Atikun yace za gina layin dogo ya hade da kowanne babban gari na kowanne jihar Najeriya, don amfanin dalibai, yan kasuwa da sauran jama’a, haka zalika ya yi alwashin sakar ma jihohi mara don su kai wani mataki na cin gashin kai.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya bayyana cewar zai baiwa jihohi damar hakar ma’adanai da kansu, tare da buda hanyoyin ruwa a Arewacin Najeriya, kamar yadda yace zai kashe makudan kudade a harkokin Ilimi, da kiwon lafiya.

Daga karshe, Alhaji Atiku Abubakar ya tabbatar da cewar zai tabbatar da karfin darajan naira, tare da samar da canjin dala na bai daya, amma fa wadannan ayyukan zasu tabbata ne idan ya zama shugaban kasar Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng